Za a Hada Atiku da Obi Su Yi Takara tare, Farfesa Utomi zai Zauna da Su

Za a Hada Atiku da Obi Su Yi Takara tare, Farfesa Utomi zai Zauna da Su

  • Farfesa Pat Utomi zai jagoranci wata tawaga wajen tattaunawa da manyan ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027
  • An shirya ganawa da Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan takarar domin tattauna yiwuwar samar da ɗan takara guda da zai wakilci haɗin gwiwa
  • Movement for Credible Elections ta ce za a gudanar da tattaunawar ne a sirrance, kuma ana sa ran kammala ganawar cikin mako biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Farfesa Pat Utomi zai jagoranci wani kwamiti na Movement for Credible Elections wajen ganawa da manyan ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa, a wani shiri na neman samar da ɗan takara guda a zaɓen 2027.

Ana sa ran ganawar za ta haɗa da Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC, Peter Obi na NDC da sauran ’yan takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Daga fara kamfen, manyan magoya bayan Tinubu suna rikici a tsakaninsu

Peter Obi da Atiku Abubakar
Peter Obi a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Mr Peter Obi|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Utomi zai gana da Atiku da Obi

Puch ta wallafa cewa MCE ta ce za a gudanar da ganawa da ’yan takarar da shugabannin jam’iyyunsu a bayan fage, kuma ana sa ran kammala shirin cikin mako biyu kafin zaman da za a gudanar a Ibadan.

Sauran ’yan takarar da ake sa ran ganawa da su sun haɗa da Adewole Adebayo na SDP, Seyi Makinde na APM, Donald Duke na PRP da Sandy Onor na PDP.

Haka kuma akwai Peter Agada na YPP da Omoyele Sowore na AAC cikin waɗanda aka shirya tattaunawa da su.

Dalilin yin tattaunawar a sirrance

Rahoto ya nuna cewa sanarwar da James Ezema, Mai Kula da Harkokin Yaɗa Labarai na MCE, ya fitar ta ce an yanke shawarar gudanar da ganawar a bayan fage ne domin kauce wa abin da ƙungiyar ta kira yiwuwar zagon ƙasa daga wasu masu adawa da shirin.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

MCE ta ce tattaunawar na da nufin kauce wa sake samun irin matsalolin da suka faru a baya, inda ’yan siyasa suka amince da buƙatar haɗa kan 'yan adawa amma suka kasa cimma matsaya kan wanda zai jagoranci ƙawancen.

Yadda za a zaɓi ɗan takara

Ƙungiyar ta ce za a gudanar da tsarin ne bisa sahihanci, gaskiya, adalci, bin ƙa’ida da samar da dama iri ɗaya ga dukkan mahalarta.

Ta ce cikin abubuwan da za a duba akwai karɓuwar ɗan takara a ƙasa, ƙwarewa, mutunci, tarihin jagoranci, manufofin siyasa da fahimtar tsarin dimokuraɗiyya.

Atiku Abubakar a gdan shi
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Haka kuma za a yi la’akari da ikon ɗan takarar na haɗa kan ’yan Najeriya da kuma yin aiki da al’ummomi daban-daban.

MCE ta ce shirin ba zai tsaya kan samar da ɗan takarar haɗin gwiwa kawai ba, domin za a kuma samar da wani tsari na gwamnati da zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro, tattalin arziki, rashin aikin yi da talauci.

Aisha Buhari ta gana da Atiku

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta ziyarci ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

DSS ta bankado shirin 'yan ta'adda na kai hare hare masallatai da coci coci

Atiku ya bayyana ziyarar a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce ya karɓi Aisha Buhari cikin farin ciki, tare da amfani da damar wajen magana kan wahalar da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Atiku ya kuma ce ’yan Najeriya na buƙatar tattalin arzikin da zai ba da damar yin aiki tukuru, samar da damammaki tare da bai wa iyalai damar rayuwa cikin mutunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng