Sarki Sanusi II Ya Dura kan Malaman Najeriya kan Shiga Harkokin Siyasa

Sarki Sanusi II Ya Dura kan Malaman Najeriya kan Shiga Harkokin Siyasa

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nemi a kara ware harkokin addini da siyasa domin shugabannin addini su mayar da hankali kan addini
  • Sanusi II ya ce ya kamata ‘yan siyasa su mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da tattalin arziki maimakon shiga harkokin addini
  • Sarkin ya kuma yi gargadin cewa siyasantar da addini da ƙabilanci na iya ƙara jefa Najeriya cikin rikice-rikice da tashin hankali a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahoto ya nuna cewa Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a kara ware harkokin addini da siyasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ka da ku": Shawarar Sanusi II ga masu son sayen hannun jarin matatar Dangote

Sanusi II ya ce ya kamata shugabannin addini su mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi addini, yayin da ‘yan siyasa za su mayar da hankali kan tafiyar da gwamnati da inganta rayuwar jama'a.

Sarki Muhammadu Sanusi a Kano
Khalifa Muhammadu Sanusi II a kan doki. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa Sanusi II ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis yayin gabatar da littafin Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era”.

Batun hada addini da siyasa

Sanusi ya ce ba aikin ‘yan siyasa ba ne su koyar da addini ga jama'a, inda ya ce aikinsu shi ne samar da ilimi, kiwon lafiya da tattalin arziki.

Ya ce ya kamata a bar harkokin addini a hannun shugabannin addini, yayin da su ma shugabannin addinin bai kamata su shiga siyasa ba.

A bayanin da ya yi, Sarki Sanusi II ya ce cakudewar harkokin addini da siyasa ta yi kamari a Najeriya.

Bambancin malamai da sanatoci

Sarkin ya ce yanzu haka babu bambanci sosai tsakanin limamai, bishop-bishop da sanatoci saboda kusan kowa ya koma ɗan siyasa.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya tuna zamansa a CBN, ya fadi babbar nadamar da ya yi

Ya ce wannan yanayi na iya rage damar shugabannin addini da sauran hukumomi wajen taka rawar da ta dace wajen sanya ido kan harkokin siyasa.

Sanusi II ya jaddada cewa ya kamata siyasa ta mayar da hankali kan abubuwan da za su inganta rayuwar jama'a da ci gaban ƙasa.

Sarki Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi II da fadawan shi. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Batun jawo rikici a siyasa

The Guardian ta wallafa cewa Sanusi II ya kuma danganta siyasantar da addini da ƙabilanci da wasu matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Ya ce matsalar ƙasar ba ta fara ne da 'yan bindiga, Boko Haram ko ta'addanci ba, sai dai ta fara ne da kalaman rarrabuwar kawuna da ake amfani da su a siyasa.

Ya ce a hankali 'yan Najeriya suka fara kallon kansu a matsayin 'yan Arewa da 'yan Kudu, Musulmi da Kirista, da kuma 'yan kabilun Hausa, Yarbawa da Igbo maimakon su fara kallon kansu a matsayin 'yan Najeriya.

Sanusi ya yi gargadin cewa idan ba a dakatar da siyasantar da addini da ƙabilanci ba, Najeriya na iya kafa tubalin sake fuskantar wani sabon tashin hankali.

Kara karanta wannan

Murtala Asada ya caccaki gwamnatin Sokoto kan rufe masallacin Sheikh Lukuwa

Nadamar Sanusi II a CBN

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanusi II ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da yake nadama a lokacin da yake gwamnan CBN, shi ne jinkirta shigar kamfanonin sadarwa cikin harkar ayyukan kuɗi.

Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da binciken 2026 kan samun damar ayyukan kuɗi a Najeriya, A2F, wanda ƙungiyar EFInA ta gudanar.

Tsohon gwamnan CBN ya ce kamfanonin sadarwa sun tanadi abubuwan za su iya taimakawa wajen faɗaɗa harkar hada-hadar kuɗi, musamman a wuraren da ba a samun isasshen sabis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng