Ana Maganar ba 'Yan Najeriya Tallafin Tsadar Fetur bayan Lita Ta kai N1,500

Ana Maganar ba 'Yan Najeriya Tallafin Tsadar Fetur bayan Lita Ta kai N1,500

  • Rahotanni sun bayyana cewa farashin man fetur ya ci gaba da tashi a sassan Najeriya dabab-daban, inda ya kai N1,500 kan kowace lita a wasu jihohi
  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin rage wa ’yan Najeriya radadin karin farashin man
  • NLC ta bukaci a biya ma’aikata tallafi, tare da sayar da danyen mai ga matatun cikin gida da Naira domin rage matsin lamba kan farashin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Farashin man fetur ya ci gaba da tashi a fadin Najeriya, inda farashin lita daya ya kai N1,500 a Kano, Yobe, Sokoto, Borno, Taraba da Zamfara.

Wannan na zuwa ne yayin da NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin rage tasirin karin farashin man fetur ga ma’aikata da sauran ’yan kasa.

Kara karanta wannan

Olu Jacobs: Abubuwan sani game da fitaccen jarumin fim da Allah ya yi wa rasuwa

'Yan kwadago da Bola Tinubu
Shugaban NLC, Joe Ajaero da tawagarsa tare da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Farashin fetur ya kai N1,500

Punch ta wallafa cewa a Yobe, mazauna Damaturu sun ce ana sayar da litar man fetur tsakanin N1,500 da N1,520 a wasu gidajen mai.

Wani mazaunin Damaturu, Hassan Auwalu, ya ce yana sayen litar man a kan N1,500, yayin da wani mai tuka keke mai kafa uku, Musa Ibrahim, ya ce yana sayen man kan irin wannan farashin a wasu gidajen mai na NNPC.

A Kano, farashin ya kai tsakanin N1,460 da N1,500 a mafi yawan gidajen mai, lamarin da ya sa wasu masu abubuwan hawa ke ajiye motocinsu saboda tsadar man.

Masu adaidaita sahu ma sun kara kudin sufuri, inda hanyar da a baya ake karbar N200 yanzu ake karbar N300, yayin da wasu dogayen hanyoyi suka kai N500 zuwa N700.

A Sokoto, litar man ta kai tsakanin N1,465 da N1,500, daga farashin N1,365 da ake sayar da ita a baya.

A Borno kuwa, man ya kai N1,500 a Maiduguri, yayin da rahotanni daga Taraba da Zamfara suka nuna cewa farashin ya kai N1,500 a wasu wurare.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Farashin litar fetur na iya haura N5000 bayan zaben 2027, an gano dalili

Maganar ba da tallafi

A wata sanarwa, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce karin farashin kudin litar man fetur ya kara jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Vanguard ta rahoto cewa NLC ta ce tashin farashin man na haifar da karin kudin sufuri, wanda hakan kan jawo karin farashin abinci, haya, kudin makaranta da sauran muhimman bukatu.

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta biya ma’aikata tallafi mai ma’ana domin rage musu radadin tsadar rayuwa.

Haka kuma ta bukaci gwamnati ta tabbatar da sayar da isasshen danyen mai ga matatun cikin gida da Naira, tare da kara karfin ajiyar man fetur na kasa domin karfafa tsaron makamashi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya na yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tashin farashin man fetur, yana mai cewa ’yan Najeriya na biyan N1,470 kan lita.

Atiku ya kwatanta farashin da na shekarar 2008, lokacin da ya ce danyen mai ya kai Dala 147 amma ana sayar da man fetur kan N65 a karkashin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.

Ta hannun babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, Atiku ya kuma nemi a binciki kudin shiga da cire-ciren Asusun Tarayya, yana mai tambayar yadda ake amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng