Rashin Imani: Yan Bindiga Sun Rutsa Sarki da Wasu Bayin Allah, Sun Masu Yankar Rago

Rashin Imani: Yan Bindiga Sun Rutsa Sarki da Wasu Bayin Allah, Sun Masu Yankar Rago

  • Wasu miyagu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe Sarkin al’ummar Luma Baale da wasu mazauna yankin a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja
  • Maharan sun ƙona wasu gidaje tare da banka wa gawarwakin wasu daga cikin waɗanda suka kashe wuta
  • Wani mazaunin yankin ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar Asabar, lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa zuwa dazuzzuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Wasu ’yan bindiga da ake zargi sun kashe basaraken al’ummar Luma Baale da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja ga hanyar yi masa yankar rago tare da wasu mazauna yankin a wani sabon hari da suka kai.

An kuma ce maharan sun cinna wa wasu gidaje wuta, tare da ƙona gawarwakin wasu daga cikin mutanen da suka kashe.

Kara karanta wannan

Ayarin Shugaba Tinubu ya jefa mutane cikin babbar matsala ta taawon lokaci a Abuja

Niger.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan bindiga sun tarwatsa mutane

Wani mazaunin Luma Baale, Mohammed Alhassan, ya shaida wa jaridar Leadership cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2026.

Magidancin ya bayyana cewa lamarin ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa dazuzzukan da ke kusa domin tsira.

“Wasu daga cikinmu sun gudu zuwa dazuzzukan da ke kusa domin tsira. Yanzu muna garin Luma inda ake da jami’an tsaro,” in ji shi.

Wadanda ake zargi da hannu a harin

Alhassan ya yi zargin cewa wasu daga cikin maharan matasan Fulani ne daga cikin al’ummar yankin, waɗanda suka haɗa kai da ’yan bindiga domin kai harin.

“An gano cewa wasu daga cikin maharan matasan Fulani ne daga ƙauyen mu, waɗanda suka haɗa kai da ’yan bindiga domin aikata wannan mummunan abu,” in ji shi.

Wannan sabon harin ya ƙara ta’azzara matsalar tsaro a Masarautar Borgu, wadda ta sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga da kuma sace mutane da dama.

Kara karanta wannan

2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna

Yadda tsaro ya tabarbarewa a Neja

An ruwaito cewa an sace ɗalibai sama da 200 daga wata makarantar Katolika da ke Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara, yayin da aka kuma sace wasu masu ibada daga wani masallaci a Dakera.

Rahotanni sun kuma nuna cewa har yanzu ’yan bindiga na tsare da ɗaruruwan mazauna yankin da suka yi garkuwa da su.

Hare-haren da ake ci gaba da kai wa sun jawo hankalin jama’a kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Masarautar Borgu, yankin da a tarihi ake danganta shi da sarautar Jagaban Borgu da aka bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ceto mutane 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su yayin wani samame a jihar Neja.

Gwarazan sojojin sun kwato makamai da kuɗi sama da Naira miliyan 4.7 a wasu hare-hare da suka kai kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a jihar Neja.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsasai bakwai na bindiga, bama-bamai uku kirar RPG, babura 33 da kuɗi Naira 4,105,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262