Sanusi II Ya Tuna Zamansa a CBN, Ya Fadi Babbar Nadamar da Ya Yi

Sanusi II Ya Tuna Zamansa a CBN, Ya Fadi Babbar Nadamar da Ya Yi

  • Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana abin da ya ce yana daga cikin abubuwan da yake nadama
  • Sarkin ya ce ya kamata kamfanonin sadarwa su samu damar shiga harkar samar da ayyukan kuɗi tun lokacin da yake gwamnan CBN
  • Sanusi II ya kuma yi magana kan yadda ya kamata a haɗa harkar kuɗi da noma, masana'antu da sauran ayyukan da ke samar da kuɗin shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, AbujaSarki Muhammadu Sanusi II ya ce yana nadamar jinkirta shigar kamfanonin sadarwa cikin harkar samar da ayyukan kuɗi a lokacin da yake gwamnan CBN.

Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da rahoton binciken 2026 kan samun damar ayyukan kuɗi a Najeriya, A2F, wanda ƙungiyar EFInA ta gudanar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Na hannun daman Tinubu ya gargadi Wike kan yawan surutu

Sarki Muhammadu Sanusi
Sarki Sanusi II a fadar shi a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Twitter

Nadamar da Sanusi ya yi

Vanguard ta wallafa cewa Sanusi II ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da yake nadama a lokacin da yake gwamnan CBN shi ne jinkirta bai wa kamfanonin sadarwa damar shiga harkar kuɗi.

Ya ce kamfanonin sadarwa sun riga sun mallaki hanyar isa ga mutane da dama, lamarin da zai iya taimakawa wajen faɗaɗa amfani da ayyukan kuɗi, musamman a wuraren da ba a samun isasshen sabis.

Ma'anar hada-hadar kuɗi

Tsohon gwamnan CBN ya ce bai kamata a auna samun damar ayyukan kuɗi kawai da yawan mutanen da suka buɗe asusun banki ko waɗanda za su iya tura kuɗi ba.

Sarki Sanusi II ya ce buɗe asusu da tura kuɗi ba ya nufin mutum ya fara samun kuɗin shiga ko kuma an fitar da shi daga talauci.

The Cable ta rahoto ya ce ya kamata a haɗa ayyukan kuɗi da tattalin arzikin zahiri, musamman noma, masana'antu da sauran harkokin da ke samar da kuɗin shiga.

Kara karanta wannan

Sokoto: Sunayen malamai da za su tantance kalaman Sheikh Musa Lukuwa kan Annabi SAW

Ya kawo misalin manoman gyada

Sanusi II ya kawo misalin manoman gyada a Kano, inda ya ce wani kamfani da ke samar da abincin maganin tamowa ga yara ta tilasta shigo da gyada daga Argentina saboda manoman cikin gida ba su samar da ita a matakin da ake buƙata ba.

Ya ce mafita ba ita ce kawai a sanya manoma cikin manhajojin hada-hadar kuɗi ta zamani ba, sai dai a horar da su, inganta yadda suke noma tare da haɗa su da masu sayen amfanin gonarsu.

A cewarsa, hada-hadar kuɗi ya kamata ta samar da alaƙa tsakanin manoma, kasuwanni da masana'antun da ke amfani da kayan da manoma ke samarwa.

bankin CBN da ke Abuja
Babban bankin Najeriya na CBN. Hoto: Central Bank of Nigeria
Source: Facebook

Bankuna sun rufe a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa bankuna a Najeriya sun rage yawan rassansu 476 tsakanin 2022 da 2025, lamarin da ya jawo raguwar wuraren hada-hadar banki da kashi 8.8 cikin 100.

Bayanan da ke cikin rahoton kididdigar harkar kuɗi na CBN na 2025 sun nuna cewa adadin rassan bankuna da cibiyoyin karɓa da fitar da kuɗi ya ragu daga 5,410 a 2022 zuwa 4,934 a 2025.

Rahotannin sun nuna cewa raguwar ta ƙara tsananta bayan 2023, inda wuraren hada-hadar banki suka ragu da 229 a 2024 sannan da wasu 210 a 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng