Binani: Cikin Jimami, Yar Takarar Gwamna Ta Sanar da Rasuwar Mahaifinta

Binani: Cikin Jimami, Yar Takarar Gwamna Ta Sanar da Rasuwar Mahaifinta

  • Tsohuwar ’yar takarar gwamnan Adamawa, Sanata Aishatu Binani, ta sanar da rasuwar mahaifinta bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a Abuja
  • Binani ta bayyana cewa mahaifinta ya rasu ne a yammacin Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2026, inda ta mika godiya ga Allah
  • An shirya gudanar da sallar jana’izar marigayin a Babban Masallacin Juma’a ranar Asabar, bayan sallar Azahar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Jihar Adamawa — An shiga jimami bayan sanar da rasuwar mahaifin tsohuwar sanata a jihar Adamawa wanda ya rasu bayan fama da jinya mai tsawo.

Yar takarar gwamnan Adamawa kuma tsohuwar Sanata, Aishatu Dahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, ta sanar da rasuwar mahaifinta.

Binani ta yi rashin mahaifinta
Yar takarar gwamnan NDC a jihar Adamawa, Aishatu Dahiru Binani. Hoto: @realaishabinani.
Source: Twitter

Sanata Binani ta sanar da rasuwar mahaifin nata ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X da safiyar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

Ta bayyana cewa mahaifinta ya rasu ne a Abuja a yammacin Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Yadda Binani ta sanar da rasuwar mahaifinta

A cikin saƙon nata, Binani ta fara da kalmar ta’aziyyar Musulunci, inda ta rubuta:

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”, wato “Lalle mu daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma.”

Duk da alhinin da take ciki na rashin mahaifinta, tsohuwar ’yar takarar gwamnan ta bayyana godiyarta ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Ta kuma rufe saƙon nata da addu’ar Allah Ya mayar da mahaifinta zuwa gare Shi cikin aminci.

Yaushe za a yi jana’izar marigayin?

Binani ta sanar da cewa za a gudanar da sallar jana’izar mahaifinta a Babban Masallacin Juma’a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, bayan sallar Azahar.

Sai dai ba ta bayyana sunan marigayin ko cikakken bayani kan musabbabin rasuwarsa ba, face cewa ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya kafin rasuwarsa a Abuja.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

Wacece Aishatu Binani?

Aishatu Binani fitacciyar ’yar siyasa ce, injiniya kuma ’yar kasuwa daga Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ta yi fice a siyasar Najeriya musamman lokacin da ta tsaya takarar gwamnan Adamawa a zaɓen 2023, tare da kasancewarta tsohuwar ’yar majalisar dattawa.

Ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasar da ake damawa da su a Adamawa, kuma ta sake nuna sha’awar shiga tseren neman kujerar gwamna a jihar.

A yanzu haka, tana neman takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin tutar jam'iyyar NDC a zaben da za a yi a 2027.

Jigon APC ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin mai kama da wannan, an ji cewa Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa, Cif Festus Oshaba-Onuh, a matsayin babban rashi ga jihar.

Marigayin, wanda aka fi sani da Ferotex, ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin mota a kan hanyar Enugu zuwa Port Harcourt.

Oshaba-Onuh shi ne daraktan kuɗi na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Enugu kafin rasuwarsa wanda aka tabbatar da cewa ya ba da gudunmawa mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.