Dalibai na cikin Alheri, Gwamnatin Tinubu Ta Waiwayo kan Masu Amfana da Shirin NELFUND

Dalibai na cikin Alheri, Gwamnatin Tinubu Ta Waiwayo kan Masu Amfana da Shirin NELFUND

  • Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) na nazarin yiwuwar ƙara tkuɗin kula da ɗalibai na wata-wata da ya kai N20,000
  • Shugaban NELFUND, Akin Sawyer, ya ce ana duba yiwuwar ƙarin tallafin ne saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita
  • NELFUND ta riga ta bayar da N180.5 biliyan a matsayin tallafin kuɗin kula da ɗalibai, yayin da ta biya N194.7 biliyan ga manyan makarantu domin kuɗin karatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Asusun ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) na nazari kan tallafin kuɗin da ke ba kowaneɗalibi da ya cancanta na wata-wata watau N20,000.

Shugaban NELFUND na kasa, Akin Sawyer, ya yi nuni da cewa ana iya ƙara kuɗin domin rage wa ɗalibai raɗaɗin tsadar rayuwa.

NELFUND.
Tambarin asusun ba da lamun ilimi na Najeriya (NELFUND) Hoto: @NELFUND
Source: Facebook

Sawyer ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Beyond the Headlines da Nifemi Oguntoye ta gabatar a gidan talabijin na TVC News ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana

NELFUND na shirin kara kudin wata

Ya amince cewa ana nazarin adadin kuɗin da ake bayarwa a halin yanzu domin la’akari da yanayin tattalin arzikin da ɗalibai ke fuskanta, amma ya ce duk wani ƙarin kuɗi zai buƙaci tsari mai kyau domin tabbatar da dorewar asusun ta fuskar kuɗi.

“Shin muna nazarin yiwuwar ƙarin kuɗin? Ƙwarai kuwa. Ana ci gaba da duba lamarin,” in ji Sawyer.

Ya bayyana cewa NELFUND na buƙatar daidaita bukatar samar wa ɗalibai ƙarin tallafin kuɗi da kuma nauyin da ke kanta na kula da yawan waɗanda ke amfana da shirin.

“Abin da ya kamata mu yi shi ne tsara lamarin ta yadda ba za mu shiga halin da ba za mu iya kula da dukkan mutanen da ya kamata mu tallafa wa ba,” in ji shi.

Tinubu na duba yiwuwar kara kudin

Ko da yake bai bayyana sabon adadin kuɗin da ake shirin bayarwa ko lokacin da za a fara aiwatar da ƙarin ba, Sawyer ya nuna cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar samar da ƙarin tallafi ga ɗalibai.

Kara karanta wannan

Shirye shiryen zaben 2027 sun kankama, INEC ta tura muhimman kayayyaki jihohi

“Na san tabbas shugaban ƙasa na duba yiwuwar shiga tsakani ta hanyar da za ta taimaka wa ɗalibai su samu isasshen abin da za su riƙa kashewa domin kammala karatunsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Ina hasashen cewa idan aka ci gaba da bibiyar wannan batu, za a ga wasu sauye-sauye a nan gaba.”

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa da ke fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ɗalibai ke kokawa kan tashin farashin abinci, sufuri, masauki da sauran muhimman abubuwan buƙata, lamarin da ya jawo tambayoyi kan ko tallafin kuɗin kula da su na wata-wata ya isa.

Alkaluman baya-bayan nan na NELFUND sun nuna cewa asusun ya raba N180.5bn ga ɗalibai a matsayin tallafin kuɗin kula da kansu tun bayan fara shirin a watan Mayun 2024.

An bude damar neman tallafin bincike

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta hannun PTDF ta gayyaci ’yan Najeriya masu bincike da su nemi tallafin ayyukan binciken man fetur da iskar gas na shekarar 2026.

Shirin ya ƙunshi fannoni takwas da suka haɗa da makamashi, fasahar zamani, kare muhalli da tattalin arzikin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262