"Aisha Buhari Ta Nuna Wanda Take Goyon baya tsakanin Tinubu da Atiku a Zaben 2027"
- Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda gabanin zaɓen 2027
- Ta kuma mara wa ɗanta, Yusuf Muhammadu Buhari, baya yayin da yake neman kujerar Majalisar Wakilai
- Yusuf na neman wakiltar mazabar tarayya ta Daura, Sandamu da Mai’Adua a Jihar Katsina a zaben 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗanta, Yusuf Muhammadu Buhari.
Yusuf Buhari na neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya domin wakiltar mazabar Daura, Sandamu da Mai’Adua a Jihar Katsina.

Source: Twitter
Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin kafafen yaɗa labarai, ne ya bayyana goyon bayan Aisha Buhari a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Tsohon sanata ya yi nadamar goyon bayan gwamna har ya hau kujerar mulki, ya nemi afuwa
Ya ce tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar ta shiga harkokin yaƙin neman zaɓe, inda take mara wa Tinubu, Radda da ɗanta baya a yunƙurinsu na siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ya rubuta cewa:
“Mai girma Aisha Buhari ta shiga shirin yaƙin neman zaɓe sosai, inda take nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Dikko Umar Radda da ɗanta, Yusuf Muhammadu Buhari, wanda ke neman zaɓen Majalisar Wakilai ta Daura, Sandamu da Mai’Adua.”
Bashir Ahmad ya wallafa wannan sako ne tare da bidiyon da aka ga Aisha Buhari sanya da doguwar riga mai dauke da hotunan Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Dikko Radda.
Yusuf Buhari na neman kujerar Majalisa
Yusuf ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta mazabar Daura, Sandamu da Mai’Adua a watan Afrilun 2026.
A cikin wasiƙar da ya rubuta wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar ne bayan shawarwari da dama.

Kara karanta wannan
Shettima ya kwatanta farin jinin Buhari da na Peter Obi, ya fadi wanda ya yi zarra
Ya kuma bayyana cewa yana son bayar da gudummawa wajen samar da shugabanci nagari, bunƙasa ababen more rayuwa da inganta rayuwar al’ummar mazabar.
A watan Afrilun 2026, wasu masu ruwa da tsaki a mazabar sun kai Yusuf gaban Gwamna Radda a gidan gwamnatin jihar da ke Katsina, inda suka bayyana goyon bayansu ga burinsa na neman kujerar Majalisar Wakilai.
Radda ya nemi a mara masa baya
A ranar 14 ga Nuwamban 2026, Gwamna Radda ya kuma yi kira ga al’ummar mazabar Daura, Sandamu da Mai’Adua da su yi la’akari da takarar Yusuf tare da mara masa baya.
Radda ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu da Radda na 2027 da aka gudanar a Makarantar Firamare ta Baure I, da ke Karamar Hukumar Baure.
Gwamnan ya bayyana Yusuf a matsayin ɗan yankin, tare da roƙon al’umma da su yi la’akari da tarihinsa da kuma goyi bayan takararsa tare da sauran ‘yan takarar APC.
Asali: Legit.ng