Tinubu Ya Koma Gida bayan Kamfen, Ƴan Uwansa Sun Shirya Masa Gata a Lagos

Tinubu Ya Koma Gida bayan Kamfen, Ƴan Uwansa Sun Shirya Masa Gata a Lagos

  • Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya isa Legas domin halartar addu’a ta musamman da iyalansa suka shirya masa
  • Tinubu ya isa Legas ne bayan kammala gangamin yakin neman zabensa na jam’iyyar APC a Ibadan, jihar Oyo
  • An shirya gudanar da addu’ar ne ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, kafin shugaban kasar ya koma birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Legas - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Legas a ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, domin halartar addu’a ta musamman da iyalansa suka shirya domin neman masa albarka.

Tinubu ya isa Legas ne bayan halartar gangamin yakin neman zabensa na jam’iyyar APC a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Asabar.

Za a yi wa Tinubu addu'a a Lagos
Shugaba Bola Tinubu yayin kamfen a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya gudanar da gangami a Oyo

An gudanar da gangamin ne a Mapo Hall, a matsayin wani bangare na yakin neman zaben shugaban kasar na sake tsayawa takara a 2027, cewar Punch.

Majiyoyi suka ce gangamin ya kasance na bakwai a ziyarar jihohi da yake yi tun bayan fara kamfen ɗin farko a Kaduna ranar 24 ga Oktoba.

Yadda aka yi kamfen Oyo cikin jimami

Tun da farko a ranar, Tinubu ya halarci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a birnin Ibadan, jihar Oyo.

Sai dai masu shirya taron sun rage armashinsa, inda suka gudanar da shi cikin yanayi na sauki, bayan wani hatsarin kwale-kwale a jihar Bayelsa ya yi sanadin mutuwar wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba tukuna.

Tinubu ya yi kamfen a Oyo
Taswirar jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Tinubu ya sauka a jihar Lagos

Shugaban kasar ya sauka ne a bangaren jiragen shugaban kasa na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, inda wasu manyan jami’an gwamnati da shugabannin APC suka tarbe shi.

Daga cikin wadanda suka tarbe shi akwai gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da tsohon gwamnan Ogun, Segun Osoba.

Haka kuma, shugabannin jam’iyyar APC, jami’an gwamnati da magoya bayan shugaban kasar sun halarci filin jirgin domin tarbar sa, cewar Vanguard.

A cewar sanarwar da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, ya fitar ranar Asabar, za a gudanar da addu’ar ne ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba.

Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran Bola Tinubu zai koma Abuja bayan kammala taron addu’ar da iyalansa suka shirya masa.

Tinubu ya yi wa yan kasa alkawari

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar.

Tinubu ya sanar da yarjejeniyar da aka kulla da kamfanin Yutong na China domin farfaɗo da tsohon kamfanin haɗa motoci wanda zai kawo ci gaba sosai a jihar.

Shugaban ƙasar ya kuma yi jimamin mutuwar mutane huɗu a hatsarin kwale-kwale a Bayelsa, tare da shirin ziyarar ta'aziyya ga iyalan wadanda iftila'in ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.