Iran: An Samu Shaidun da ke Nuna Trump Ya Aikata Babban Laifi a Duniya
- Kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce akwai shaidu masu ƙarfi da ke nuna Amurka ta tafka laifukan yaƙi ta hanyar kai hari makaranta
- Rahoton ya kuma gano cewa hukumomin Iran sun aikata laifuffukan cin zarafin ɗan adam yayin murƙushe zanga-zangar ƙasar da aka yi a farkon wannan shekarar
- Harin da gwamnatin Donald Trump ta kai kan makarantar Minab ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150, ciki har da yara ɗalibai kimanin 120 a kasar Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Geneva – Wani kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Ɗinkin Duniya game da kasar Iran ya bayyana a ranar Alhamis cewa yana da kwararan shaidu na yarda cewa ƙasar Amurka ce ke da alhakim kai hare-haren soji a Iran.
Haka zalika, kwamitin ya gano cewa hukumomin Iran sun aikata laifuffukan cin zarafin ɗan adam yayin murƙushe zanga-zangar adawa da gwamnati ta hanyar amfani da ƙarfin soja.

Source: Getty Images
Reuters ta ruwaito cewa rahoton da kwamitin ya shirya domin mika wa Hukumar Haƙƙoƙin Ɗan Adam da ke Geneva, ya binciki ayyukan dakarun Amurka a yaƙin da ya barke a watan Fabrairu da kuma martanin Iran ga zanga-zangar ƙasar.
Harin da aka kai Minab
Masana na majalisar sun bayyana cewa dakarun Amurka ne ke da alhakim harin da aka kai wa makarantar firamare ta Shajareh Tayyebeh da ke birnin Minab, inda mutane sama da 150 suka rigamu gidan gaskiya, ciki har da yara ɗalibai 120.
CBC ta rahoto cewa hukumar ta Kammala cewa:
"Amurka ta kai harin ne kan gini na makaranta yayin da take sane da babban haɗarin kai hari cibiyar farar hula kuma ta gudanar da aikin cikin sakaci ba tare da kula da yiwuwar faruwar hakan ba. Harin ya zama laifin yaƙi ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa."
Me ake zargin Iran ta yi?
Binciken ya kuma gano cewa hukumomin Iran sun gudanar da hare-hare na zalunci a kan fararen hula yayin zanga-zangar da ta barke a ƙarshen watan Disamba, wanda ya ƙunshi kisa mara ka'ida, azabtarwa da sauransu.
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa mutane 3,038 ne suka mutu yayin da 25,000 suka ji rauni, sai dai kwamitin ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya fi haka yawa nesa ba kusa ba.

Source: Getty Images
Ita ma Amurka an zarge ta da kai wani harin makamancin wannan kan wani cibiyar wasanni a garin Lamerd wanda ya kashe mutane 22, sannan dakarun CENTCOM sun ƙana kai harin.
Batun dakatar da yaki da Iran
A wani labarin daban, kun ji cewa majalisar Amurka ta nemi kawo ƙarshen yaƙin da Amurka ke yi a Iran, ta hanyar amincewa da ƙudurin ikon yaƙi wanda ke hana Shugaba Donald Trump ci gaba da aiki da sojoji.
Sakamakon ƙuri'ar da aka kaɗa na 220-204 ya sami goyon bayan wasu 'yan jam'iyyar Republicans da suka haɗa kai da 'yan jam'iyyar Democrats domin tsayar da yaƙin.
Dan majalisa Zach Nunn na jam'iyyar Republican ya bayyana cewa "a halin yanzu fagen tattaunawa ya rufe, don haka ci gaba da amfani da ƙarfin soji yana buƙatar izinin majalisa, saboda ba zan goyi bayan yaƙin da ba shi da iyaka ba."
Asali: Legit.ng

