An Dauki Bidiyon Matar Aure na Jima'i da Kare, an Kama Ta

An Dauki Bidiyon Matar Aure na Jima'i da Kare, an Kama Ta

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Florida a Amurka ta kama wata mata mai shekaru 38 biyo bayan zarginta da aikata fasikanci da kare
  • Rahoto ya nuna cewa mijin matar ya gano lamarin ne ta hanyar bidiyon kyamarar tsaro da ya kafa domin gano mai satar kudi a gidan
  • Bayan kama ta da ya ce ya yi, mijin ya mika bidiyon da hotunan ga jami'an tsaro wanda hakan ya kai ga tsare matar a gidan yari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Florida – Jami'an 'yan sanda a jihar Florida ta ƙasar Amurka sun kama wata mata mai suna Malia Nummerdor, sakamakon zarginta da aikata laifuffukan badala da karen gidansu.

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da matar mai shekaru 38 ne a kotu biyo bayan korafin da mijinta ya fitar a shafinsa na Facebook game da mummunan al'amarin.

Kara karanta wannan

Murtala Asada ya caccaki gwamnatin Sokoto kan rufe masallacin Sheikh Lukuwa

Wani kare a Amurka
Wani kare a jihar Los Angeles a Amurka da aka ceto yayin gobara. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar labarai ta New York Post ta ruwaito cewa mijin matar ya bayyana cewa yana da shaidar hotuna da bidiyo na abin da ya faru sakamakon kyamarorin tsaro da ya sanya a gidan su.

Yadda aka gano matar a Florida

Binciken 'yan sanda na ofishin sheriff na yankin Charlotte County ya nuna cewa mijin ya kafa kyamarorin ne a gidan domin gano wanda ke satar kuɗi daga cikin mazubin tsabar kuɗi.

Yayin da yake duba rahotannin kyamarar da ke ɗakin barci, sai ya ci karo da bidiyon matar tasa tana aikata badala da karen gidansu.

Yahoo News ta ruwaito cewa jami'an tsaro na cewa:

"Mijin ya nuna wa masu bincike hotunan da aka ɗauko daga bidiyon tare da ba su damar amfani da kwamfutarsa domin samun ainihin bidiyon a matsayin shaida."

Raddin matar da kama ta

Yayin da 'yan sanda suka yi tambayoyi ga Nummerdor a ranar Talata, ta amince cewa ita ce a cikin bidiyon, amma ta ƙaryata aikata laifin saduwa da karen inda ta ce kawai shafa shi take yi.

Kara karanta wannan

Daukar doka hannu: Matasa sun kashe tsoho dan shekara 80 bisa zargin aikata maita

'Yan sanda sun ce bayar da amsoshinta ya kasance lamari mai cin karo da juna gami da rashin gamsarwa, wanda hakan ya kai ga kama ta tare da rufe ta a gidan yarin Charlotte County.

Taswirar jihar Florida
Taswirar jihar Florida a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wasu rahotanni sun nuna cewa hukumomi kasar Amurka za su cigaba da gudanar da bincike game da zargin da aka yi wa matar domin gano gaskiya da daukar matakin da ya dace.

An hana Abbas zuwa amurka

A wani labarin daban, kun ji cewa gwamnatin ƙasar Amurka ta sake hana Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, bizar shiga ƙasar domin halartar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a birnin New York.

Ma'aikatar Wajen Amurka ta bayyana cewa matakin ya shafi jami'an ƙungiyar PLO da na gwamnatin Falasɗinu (PA) saboda "gazawarsu wajen cika alƙawuran sauye-sauye".

Wannan matakin ya tilasta wa shugaban gudanar da jawabi ta hanyar sadarwar bidiyo kamar yadda ya aikata a taron shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng