Trump Ya Yi wa Shugaban Falasdinawa Wulakanci kan Shiga Amurka
- Amurka ta sake hana Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas bizar shiga ƙasarta domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York
- Ma'aikatar Wajen Amurka ta bayyana cewa matakin ya shafi jami'an PLO da PA sakamakon rashin cika alƙawuran sauye-sauye
- Wannan mataki na Amurka ya sa ta saɓa wa ƙasashe da dama da suka haɗa da Faransa waɗanda suka amince da ƙasar Falasɗinu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
New York – Wata majiya mai tushe ta bayyana a ranar Laraba cewa gwamnatin ƙasar Amurka ta hana Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, bizar shiga ƙasar domin halartar taron Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a New York.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar wajen ƙasar ta fitar wadda ba ta ambaci sunan Abbas kai tsaye ba, Amurka ta ce za ta hana jami'an ƙungiyar ƴancin Falasɗinu (PLO) da na gwamnatin Falasɗinu (PA) biza sakamakon "gazawarsu."

Source: UGC
Hukumar labarai ta AFP ta ruwaito wata majiya mai tushe tana tabbatar da cewa wannan mataki ya shafi shugaban na Falasɗinu, Mahmoud Abbas.
Dalilan da Amurka ta bayar
Gwamnatin Amurka ta ɗauki irin wannan mataki a shekarar da ta gabata, inda ta tilasta wa shugaban gudanar da jawabi ta kafar bidiyo.
Amurka ta zarge su da tura maganar zuwa kotunan ƙasa da ƙasa irin su ICC da ICJ.
BBC ta wallafa cewa sanarwar Amurka ta ce:
"Ƙungiyoyin PLO da PA sun sake gazawa wajen cika alƙawuran da suka ɗauka. Wannan ya haɗa da ɗaukar matakai a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da suka saɓa wa yarjejeniyoyin baya, da ƙoƙarin tsallake tattaunawa ta hanyar neman amincewa ta ɓangare ɗaya."
Batun saɓani da ƙasashen duniya
Wannan matakin ya sa Amurka ta saɓa wa ƙasashe da dama, har da ƙasar Faransa, waɗanda suka amince da 'yancin ƙasar Falasɗinu a Majalisar Ɗinkin Duniya a shekarar da ta gabata.
Sama da mambobi 142 na Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka goyi bayan amincewa da ƙasar Falasɗinu sakamakon taron tsarin ƙasashe biyu da Faransa da Saudi Arabia suka jagoranta.

Source: Getty Images
Rikicin na faruwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar tashe-tashen hankula da hare-haren dakarun Isra'ila a yankin West Bank tun bayan barkewar yaƙin Gaza.
Barnar da Iran ta yi wa Amurka
A wani labarin daban, kun ji cewa hotunan da aka fitar kwanan nan sun nuna irin gagarumar lalacewar da hare-haren ƙasar Iran suka yi wa wurare da cibiyoyin sojojin Amurka daban-daban a yankin Gabas Tsakiya.
Hotunan da sojojin da ke bakin daga suka fitar sun nuna yadda aka ruguza gine-gine, sansanoni, da cibiyoyin sadarwa a ƙasashe irin su Saudi Arabia da Kuwait.
Ɗaya daga cikin sojojin ya nuna damuwarsa bisa yadda gwamnatin Amurka ke ɓoye ainihin asarar da aka tafka a sansanonin nata ba tare da sanar da jama’ar ƙasar ba.
Asali: Legit.ng

