An Fadi Adadin Kuri'un da Tinubu zai Samu yayin da ake Shirin Hada Atiku da Obi
- Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai samu akalla kashi 65 na ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen 2027
- Jibrin Kofa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai inda ya ce Tinubu ya ƙara samun karɓuwa a tsakanin ’yan Najeriya
- Ɗan majalisar ya kuma bayyana Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin wani muhimmin ɗan siyasa da ya taimaka wa jam’iyyar APC da gwamnatin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu akalla kashi 65 na jimillar ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da wasu 'yan gwagwarmaya suka kaddamar da tafiyar 'Tinubu Must Go' domin kawar da gwamnatin APC a zaben 2027.

Source: Twitter
Jibrin Kofa ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026.
'Tinubu ya ƙara samun karɓuwa'
Ɗan majalisar ya ce Tinubu ya ƙara samun karɓuwa a tsakanin ’yan Najeriya, yana mai cewa hakan zai taimaka wa shugaban ƙasar a zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa Jibrin Kofa ya kuma ce Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne, ba shi da tarihin shan kaye a zaɓe a siyasar shi.
Magana kan Wike da 'yan APC
Jibrin ya bayyana Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin wani muhimmin mutum ga APC, yana mai cewa tsohon gwamnan Rivers ya yi sadaukarwa wajen tallafa wa Tinubu da jam’iyyar.
Jibrin ya yi kira ga gwamnonin APC da su ɗauki Wike a matsayin ɗaya daga cikinsu, duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP.
Ya ce bai kamata a rika kallon Wike a matsayin wanda yake wajen tsarin siyasar jam’iyyar ba saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga gwamnatin Tinubu da kuma manufofin da suka shafi zaɓen 2027.

Source: Twitter
Kalaman Jibrin sun zo ne yayin da ake ci gaba da samun muhawara kan dangantakar Wike da wasu gwamnonin APC gabanin zaɓen 2027.
Martanin 'yan Najeriya
Bayan kalaman Jibrin Kofa, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan hasashen da ya yi.
Wasu sun nuna amincewa da kalaman, yayin da wasu suka yi musu suka tare da cewa sakamakon zaɓe ne kawai zai nuna irin goyon bayan da Tinubu zai samu.
Batun hada Atiku da Obi
A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Pat Utomi ya jagoranci wani shiri na Movement for Credible Elections da ke neman haɗa manyan ’yan adawa domin samar da ɗan takara guda a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shirin ya ƙunshi tattaunawa da ’yan takara da shugabannin jam’iyyunsu, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Adewole Adebayo, Seyi Makinde, Donald Duke, Sandy Onor, Peter Agada da Omoyele Sowore.
MCE ta ce tattaunawar za ta gudana ne a bayan fage domin samar da tsarin da za a bi wajen zaɓar ɗan takara guda, tare da samar da wata manufa ta bai ɗaya kan batutuwan da suka shafi Najeriya.
Asali: Legit.ng

