An Fara Bincike kan Mutuwar Mutum 33 a Hannun Hukumar Najeriya
- Hukumar NSCDC ta fara bincike kan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ne a Jihar Neja
- Mutanen sun mutu ne bayan an kama su yayin samamen dakile haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da aka gudanar a M.I. Wushishi/Lukoto
- Har yanzu ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwar mutanen ba, an ce zargin wata cuta ce ta haddasa mutuwar bai tabbata ba tukuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya, NSCDC, ta fara bincike kan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ne a hannunta a Jihar Neja.
An kama mutanen ne yayin samamen da rundunar NSCDC ta Jihar Neja ta gudanar a yankin M.I. Wushishi/Lukoto a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026.

Source: Twitter
Mutum 33 sun mutu
Punch ta wallafa cewa lamarin ya biyo bayan rahotannin cewa akalla mutane 33 da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ne sun mutu bayan an tsare su a wani wurin tsarewa na NSCDC a Minna.
An gano mutuwar mutanen ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, inda Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, ya danganta lamarin da zargin barkewar wata cuta.
Sai dai hedikwatar NSCDC ta ce har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwar ba, tana mai cewa duk wani rahoto da ya danganta mutuwar da wata takamaiman cuta na jiran tabbatarwa daga likitoci da dakunan gwaje-gwaje.
An kafa kwamitin bincike
Kwamandan Janar na NSCDC, Ahmed Abubakar Audi, ya bayar da umarnin kafa tawagar bincike mai ƙarfi domin gano abubuwan da suka kai ga mutuwar mutanen.
Tawagar, wadda Mataimakin Kwamandan Janar mai kula da Leken Asiri da Bincike zai jagoranta, za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Binciken zai duba halin da mutanen suke ciki lokacin da aka kama su, tsawon lokacin da suka yi a tsare, yanayin wurin da aka tsare su da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su.
Dalilin mutuwar mutanen
Hukumar ta ce za ta guji yin zato kan musabbabin mutuwar har sai an kammala binciken lafiya da na dakunan gwaje-gwaje.
NSCDC ta ce rahotannin da ke cewa wata takamaiman cuta ce ta haddasa mutuwar ba su samu cikakken tabbaci ba a yanzu.
Hukumar ta kuma bayyana alhininta ga iyalan mutanen da suka mutu, tare da tabbatar musu cewa za a binciki lamarin dalla-dalla kuma a ɗauki matakin da ya dace bisa hujjojin da bincike ya tabbatar.

Source: Original
Audi ya kuma umarci jami'an hukumar da su ba da fifiko ga lafiyar jiki da jin daɗin duk mutanen da ke hannun hukumar a halin yanzu.
The Cable ta wallafa cewa ya kuma bayar da umarnin ɗaukar matakan kare jami'an da ka iya yin hulɗa da mutanen da abin ya shafa.
NLC ta yi korafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta amincewa da tallafin gaggawa ga ma'aikata a faɗin ƙasar.
NLC ta buƙaci a samar da tallafin albashi ga ma'aikata tare da ware ɗanyen man fetur ga matatun mai na cikin gida da Naira domin rage tasirin tsadar man fetur.
Ƙungiyar ta kuma nemi gwamnati ta ƙara yawan wuraren ajiyar man fetur na ƙasa domin shirin tunkarar matsalolin makamashi da kuma ƙarfafa tsaron makamashi.
Asali: Legit.ng


