Saudiyya Ta Koma China bayan Trump Ya Ki kai Hari kan Houthi, Iran Ta Magangu
- Rahtoto ya nuna cewa kasar China ta nemi Iran ta yi amfani da tasirinta wajen rage hare-haren kungiyar Houthi da ke Yemen
- Matakin ya biyo bayan roƙon Saudiyya ga China, yayin da Houthi ke samun ci gaba a gabar Tekun Bahar Maliya da kusa da Bab el-Mandeb
- China ta ce tana son a dakatar da yaɗuwar rikicin zuwa hanyoyin jigilar makamashi da harkokin sufuri da take dogaro da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Dubai – Kasar China ta nemi Iran ta yi amfani da tasirinta wajen shawo kan kungiyar Houthi ta Yemen bayan Saudiyya ta nemi taimakon Beijing.
Matakin ya zo ne yayin da kungiyar Houthi ke samun ci gaba cikin sauri a gabar Tekun Bahar Maliya da kuma yankin mashigar Bab el-Mandeb, lamarin da ya ƙara sanya fitar da man Saudiyya da jigilar kayayyaki cikin haɗari.

Source: Getty Images
Reuters ta rahoto cewa wasu majiyoyi uku daga Iran da suka san abin da ya faru ne suka bayyana hakan, amma suka nemi a ɓoye sunayensu.
China ta yi wa Iran magana
Majiyoyin sun ce China ta aika da saƙon sirri ga Tehran, inda ta nemi Iran ta yi amfani da tasirinta kan Houthi domin hana rikicin yaɗuwa zuwa wasu sassan yankin.
Tun da farko dai China ta yi kira da a yi haƙuri, a gudanar da tattaunawa sannan a dawo da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.
Sai dai majiyoyin sun ce saƙon da Beijing ta aika a sirrance ya wuce abin da ta bayyana a bainar jama'a, saboda damuwarta kan hanyoyin makamashi da take dogaro da su.

Source: Getty Images
Iran ta mayar da martani
Majiyoyin sun ce ba a bayyana yadda China ta isar da saƙon ga Iran ba, ko kuma ko an isar da shi yayin ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya kai China ranar Laraba.
Sun ce martanin Tehran shi ne cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin sun dogara ne da kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.
Times of Israel ta wallafa cewa jami'an China ba su yi wata barazana kai tsaye ba ko kuma nuna cewa za su matsa wa Iran ta fuskar tattalin arziki idan ba ta yi amfani da tasirinta kan Houthi ba.
Sai dai a'aikatar Harkokin Wajen China ta shaida cewa ba ta son ganin rikicin yankin ya ƙara yaɗuwa zuwa Yemen da Bahar Maliya.
An zargi Amurka kan Iran
A wani rahoto, kun ji cewa Majalisar Ɗinkin Duniya kan haƙƙin ɗan Adam sun ce akwai dalilai masu ƙarfi da ke nuna cewa Amurka ta aikata laifuffukan yaƙi a hare-hare biyu da aka kai Iran.
Rahoton wata tawaga mai zaman kanta ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan wata makarantar firamare a Minab da wani filin wasanni a Lamerd.
Amurka ta musanta kai hari kan Lamerd, yayin da ta ce tana binciken abin da ya faru a Minab. Wata jami'ar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kuma ce ƙasar ba ta amince da sakamakon binciken ba.
Asali: Legit.ng

