'Asirina Zai Tuno': Gwamna Ya Ce Zai Shiga Matsala idan Tinubu Ya Faɗi Zaɓe
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ce zai rasa karfin siyasa idan Shugaba Bola Tinubu bai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027 ba
- Okpebholo ya kwatanta kansa da ’yan kalangu da ke rawa bisa kidan wani, yana mai cewa Tinubu ne ke taimaka masa a siyasance
- Gwamnan ya sake nanata alkawarin samar wa Tinubu kuri'u miliyan 2.5 daga Edo, duk da cewa a 2023 Peter Obi ya lashe jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa zai kare a siyasa idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyyar APC a wani gangamin neman goyon bayan sake zaben Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Gwamna ya roki a zabi Tinubu
Okpebholo ya kwatanta kansa da wani dan wasan kwaikwayo da ke rawa yayin da wani ke buga masa kida, yana mai cewa karfinsa na siyasa ya dogara da mutumin da ke mara masa baya, cewar ThisDay.
A cikin kalamansa da ya yi da harshen Pidgin, gwamnan ya ce:
"Ku gaya mini, kun san abin rufe fuskar nan da ake rawa da shi? A baya lokacin da na zo wurinku, kun fito da shi yana rawa sosai. Me ke sa shi rawa? Ba wai akwai wanda ke buga masa kida ba ne?"
Ya ci gaba da cewa:
"Saboda haka, akwai wanda ke mara mini baya, idan wannan mutumin ya bar mulki, to karfina ya kare."
Gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ne yake mara masa baya, yana mai cewa ba ya fadin karya idan ya yi alkawarin aiwatar da wani abu.
Ya ce:
"Kun san ba na karya. Idan na ce zan yi wani abu, haka yake faruwa. Baba Tinubu ne, shi ne yake mara mini baya."

Source: Original
Matsayar gwamnan a baya kan Tinubu
A kwanakin baya ma, Okpebholo ya bayyana irin wannan matsaya yayin kaddamar da reshen Edo na kungiyar PBAT Door-to-Door Campaign Movement.
A lokacin, gwamnan ya ce yana gudanar da ayyukansa ne saboda Shugaba Tinubu yana bayansa, don haka dole ne shugaban ya ci gaba da zama a kan mulki bayan zaben 2027.
Ya kara da cewa ci gaba da ayyukan raya jihar Edo ya dogara da kasancewar Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, cewar Punch.
Alkawarin kuri'u miliyan 2.5
Gwamnan ya sha alwashin samar wa Tinubu kuri'u miliyan 2.5 daga jihar Edo a zaben 2027, inda ya bayyana cewa babu abin da zai sauya wannan matsaya.
Sai dai alkaluman masu rajistar zabe a jihar sun nuna cewa akwai tsakanin mutane miliyan 2.8 zuwa miliyan 2.865 da suka yi rajistar zabe.
A zaben shugaban kasa na 2023, Tinubu ya samu kuri'u 144,471 a Edo, yayin da dan takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya lashe jihar da kuri'u sama da 331,000.
Gwamna ya yi wa Tinubu alkawari
An ji cewa Kassim Afegbua ya ce burin samun ƙuri’u miliyan 2.5 ga Tinubu a Edo abu ne mai yiwuwa, bisa yawan masu rajistar zaɓe a jihar.
INEC ta ƙiyasta yawan masu rajistar zaɓe a Edo zuwa miliyan 2.865, kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
Gwamna Monday Okpebholo zai zagaya kananan rumfunan zaɓe 192 domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


