Dattawa Sun Shiga Magana, Ana Ta Tir da Sakin Auren Gwamna Abba a Jihar Kano
- Dr. Hakeem Baba Ahmed ya nuna takaicinsa game da yadda siyasa ta gurbace yau a yankin Arewacin Najeriya
- Tsohon kakakin na kungiyar dattawan Arewa ta ACF ya ce Gwamnan Kano bai kyauta da ya saki matarsa a fili ba
- Shugaban jam’iyyar PRP yana so a ga bayan APC, amma bai yi na’am da yi wa Bola Tinubu ihu a masallaci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hakeem Baba Ahmed ya yi Allah-wadai da abin da Gwamnan jihar Kano ya yi na sakin uwar ‘ya ‘yansa a wajen taro cikin bainar jama’a.
Dr. Hakeem Baba Ahmed yana ganin babu abin da zai sa auren Abba Kabir Yusuf da Zainab Musa Kwankwaso ya zo a karshe a irin wannan yanayi.

Source: Facebook
Hakeem Baba Ahmed ya soki Gwamnan Kano
Hakeem Baba Ahmed wanda yana cikin dattawan yankin Arewacin Najeriya ya bayyana matsayarsa a wata hira da tashar DCL Hausa ta yi da shi.
Tsohon hadimin shugaban kasar ya yi watsi da zancen da ake yi cewa zaurance gwamnan ya yi, bai fito karara ya fada wa duniya ya saki matarsa ba.
Dr. Hakeem yana ganin kalaman gwamnan sun nuna inda ya dosa, yana mai koka wa game da yadda siyasar ta lalace kuma har tana bata ibada.
Hakeem Baba Ahmed ya ce:
"Yanzu gwamna ya fito ya fada wa jama’a, na saki mata ta, an nemi in saki na saki. Suna da ‘ya ‘ya shida, jama’a Allah!
Da yake magana, ya tuna wa duniya muhimmancin mu’amalar aure wanda Musulunci ya yi tanadin dokokin zama da kuma yadda ake tsinka igiyar.
Ya nuna bai daidai ba ne gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin taron jama’a, yana magana tamkar na kamfe ya sanar da su cewa ya rabu da mai dakinsa.
“Ina ruwan siyasa da zaman aurenka. Ina ruwan mutanen da suka zo taron siyasa da kawo masu irin wannan.”
- Hakeem Baba Ahmed
An zargi Gwamna Abba Kabir da sabon Allah
Da aka tambaye shi wani mataki zai dauka da a ce Mai girma Abba Kabir ‘dan PRP ne, sai ya ce ai gwamnan ba jam’iyyarsa ta APC ya yi wa laifi ba.
“Ai ba jam’iyya ya yi wa laifi ba. Allah ya yi wa laifi.
Shugaban PRP na kasan ya cigaba da cewa kuma ya kamata Abba ya san laifin wanda ya keta mutuncin aure domin abin da ya yi sam ba daidai ba ne.
Yake cewa a matsayin musulmai, sun yi imani akwai ranar da mutum zai tsaya gaban Allah SWT.
Hakeem bai ji dadin yin ihu a masallaci ba
A hirar, tsohon shugaban na APC a Kaduna ya kuma sake yin tir da yadda wasu suka maida masallaci wajen tada hayaniya a maimakon yin ibada.
Hakeem ya yi wannan magana ne ganin wasu sun yi wa Shugaba Bola Tinubu ihu yayin da ya ziyarci wani masallaci domin yin sallar Juma’a a birnin Abuja.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa
‘Dan siyasar yana goyon bayan yin waje da Tinubu a filin zabe, amma bai ga dacewar a rika yin munanan kalamai a wuri mai daraja kamar masallaci ba.
Nafisa Kwankwaso ta caccaki Abba Kabir a Facebook
Kuna da masaniya cewa Nafisa Kwankwaso ba ta raga wa Abba Kabir Yusuf ba, ta yi masa gorin alherin da aka yi masa kafin ya shiga fadar mulki.
Tsohuwar surukar gwamnan jihar Kano ta yi masa kaca-kaca a shafin Facebook, ta ke cewa bai nuna halaccin duk alherin da aka yi masa a baya.
Nafisa ta soki yadda Abba ya rabu da Zainab Kwankwaso tana tuna masa tulin yara mata da ya haifa da kuma alakar da ke tsakaninta da mahaifiyarsa.
Asali: Legit.ng

