Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Yi Barazana kan Zaben 2027 a Najeriya
- Rahoton SARI Global ya ce shugaban ’yan bindiga a Anka ya gargaɗi shugabannin al’umma cewa ba za a bari a gudanar da zaɓe a yankunansu ba
- ’Yan bindiga sun toshe manyan hanyoyi a Zamfara, sun ƙona motoci tare da kakaba wa al’ummomin Dansadau harajin Naira miliyan 50
- Zamfara ta zama jiha mafi yawan hare-haren tsaro a Najeriya a watan Oktoba 2026, inda aka samu hare-hare 69 da mutuwar mutum 137
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wasu jagororin ’yan bindiga a jihar Zamfara sun shaida wa shugabannin al’umma a ƙaramar hukumar Anka cewa ba za su bari a gudanar da zaɓe a yankunansu ba.
Wani rahoto da kamfanin nazarin bayanan tsaro na SARI Global mai rajista a Amurka ya fitar ne ya bayyana hakan.

Source: Facebook
Rahoton mai taken Nigeria Monthly Security Overview for October 2026, wanda jaridar The Punch ta samu ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa Zamfara ta maye gurbin Borno a matsayin jiha mafi yawan hare-haren tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan
"Tinubu bai fi ya lashe jihohi 2 ba"; An yi sabon hasashe kan zaben shugaban kasa
’Yan bindiga sun yi barazanar hana gudanar da zaɓe
Rahoton ya ce barazanar ta zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ’yan bindiga ke ƙara tsaurara toshe manyan hanyoyin jihar, ƙona motoci da kuma kakaba wa al’ummomin gundumar Dansadau harajin Naira miliyan 50.
Haka kuma, matakan sun tilasta wa fiye da mutum 300 barin gidajensu.
A watan Oktoba kaɗai, an samu hare-hare 69 a Zamfara, inda mutane 137 suka rasa rayukansu.
Rahoton ya ce shugaban ’yan bindiga ya tara shugabannin al’umma a Anka a watan Oktoba, inda ya sanar da su cewa ba za a gudanar da zaɓe a yankunansu ba.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a kawo ƙarshen toshe hanyoyin ba, yankunan da abin ya shafa za su iya zama wuraren da ba za a iya gudanar da ayyuka cikin ’yanci ba, lamarin da zai iya tilasta wa jama’a ƙaura har abada.
An ƙara tsaurara toshe hanyoyi da kai hare-hare

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
SARI Global ta bayyana cewa ayyukan ’yan bindiga a Zamfara sun sauya daga kai hare-haren kwanton bauna zuwa tsarin mamaya da sarrafa manyan hanyoyi.
A ranar 13 ga Oktoba, wata ƙungiyar ’yan bindiga ta fitar da bidiyo tana barazanar ƙona duk motar da ta bi hanyar Gusau zuwa Dansadau.
Washegari, an ƙona wata babbar mota a ɓangaren hanyar Dansadau zuwa Magami. A ranar 16 ga Oktoba kuma, ’yan bindigar sun tare hanyar, sun lalata motoci tara tare da dauke kayayyakin matafiya.
Rahoton ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun yi barazanar kai hari kan al’ummomin da suka ƙi biyan harajin Naira miliyan 50.
Haka kuma, a ranar 8 ga Oktoba, an gano wasu bama-bamai biyu da aka ƙera cikin gida a hanyar Magami zuwa Hannutara zuwa Dansadau.
An tare hanyoyi da dama, an kashe matafiya
Rahoton ya ce toshe hanyoyin bai tsaya kan hanya guda ba, domin ’yan bindigar sun kuma rufe hanyoyin Gurusu zuwa Anka, Abare zuwa Anka, Gusau zuwa Magami, Kaura Namoda zuwa Shinkafi, Mayanchi zuwa Anka, Anka zuwa Kuturu da Maradun zuwa Danbaza.
A wasu lokutan, sun yi garkuwa da matafiya tare da kashe direbobi da manoma.
SARI Global ta ce rakiyar jami’an tsaro ba ta wadatar wajen kare matafiya ba. A ranar 11 ga Oktoba, wani kwanton bauna da aka kai kusa da Gurusu ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 20.
Waɗanda suka mutu na cikin ayarin motocin ’yan kasuwa da jami’an tsaro ke rakawa, ciki har da sojoji da ’yan sanda.
A ranar 21 ga Oktoba, dakarun soji sun sake buɗe hanyar Gusau zuwa Dansadau tare da fara kai wa matafiya rakiya a kai a kai.
Sai dai ’yan bindigar sun sake tare hanyar a ranar 31 ga Oktoba.
Rahoton ya yi hasashen ƙarin mamaye yankuna
A hasashensa kan yadda matsalar tsaron za ta kasance, SARI Global ta ce ƙungiyoyin ’yan bindiga na iya ƙara ƙarfafa ikonsu a yankin Kuyambana, tare da yawaita amfani da bama-bamai da aka ƙera cikin gida.
A faɗin Najeriya kuwa, rahoton ya ce adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ya ninka a watan Oktoba, inda ya tashi daga mutum 27 a watan Satumba zuwa 55.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin
Kamfanin ya kuma bayyana cewa yanayin siyasa ya ƙara tsananta a yankunan Arewa, inda aka samu kusan al’amura 46 da suka shafi jam’iyyun siyasa, kamfen ko ’yan daba.
Rahoton ya ce an yi wa masu yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki jifa a aƙalla jihohi biyar.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga da ake zargi sun kashe basaraken al’ummar Luma Baale da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja tare da wasu mazauna yankin a wani sabon hari da suka kai.
An kuma ce maharan sun cinna wa fadar sarkin da wasu gidaje wuta, tare da ƙona gawarwakin wasu daga cikin mutanen da suka kashe.
Asali: Legit.ng
