Ribadu, Dikko Radda da Mutum 10 da Tinubu Ya Manta da Su a Kwamitin Yakin Zabe

Ribadu, Dikko Radda da Mutum 10 da Tinubu Ya Manta da Su a Kwamitin Yakin Zabe

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da kwamitin mutane 223 da za su taya shi aikin yakin neman tazarce a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Duk da yawan mutanen da suke cikin majalisar kamfen, akwai wasu fitattun ‘yan siyasa kuma ‘yan APC da kamar an manta da su.

Rahotonmu ya maida hankali wajen tattaro manyan APC da babu sunansu a cikin kwamtin yakin neman zaben shugaban kasar.

Abba Kabir Yusuf da Dikko
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Dikko Radda ba su da wuri a kwamitin kamfen APC Hoto: Abba Kabir Yusuf/Dikko Ummaru Radda
Source: Facebook

'Yan APC da ba su a kwamitin kamfe

1. Simon Lalong

Duk da shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu a 2023, wannan karo gaba daya babu sunan tsohon gwamnan.

Ban da kasancewarsa tsohon Darekta janar a kamfe, Solomon Lalong ya yi minista a gwamnatin Tinubu, a yanzu kuma sanata ne.

2. Yahaya Bello

Da aka yi zaben da ya wuce, wanda ya jagoran matasa na kasa wajen tallata jam’iyyar APC shi ne tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

A zaben wannan karo, gaba daya babu labarin matashin ‘dan siyasa a cikin majalisar kamfe duk da irin tasirin shi musamman a jiharsa.

3. Festus Keyamo

Lokacin da Muhammadu Buhari yake neman ya zarce a mulki, Festus Keyamo SAN ya zama kakakin kwamitin yakin neman zaben APC.

Keyamo ya rike kujerar Darektan sadarwa na musamman a kamfe. The Will ta rahoto shi cikin wadanda ba su cikin majalisar yakin 2027.

4. Gbenga Daniel

Wasu sun yi tunanin Gbenga Daniel zai iya bada gudumuwa wajen kai APC ga nasara musamman saboda ba zai rasa sanin sirrin 'yan adawa ba.

Atiku Abubakar ya dauko shi ya zama shugaban kwamitin yakin neman zaben 2019 amma daga baya ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.

5. Ibikunle Amosun

Wani tsohon gwamna da bai cikin kwamitin tallata takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima shi ne sanatan Ogun ta tsakiya, Ibikunle Amosun.

Da aka yi zaben gwamnoni a 2019, Amosun bai goyi bayan APC ba. Amma a 2023 Darektan kamfe ne a harkar tattarowa Tinunu/Shettima jama’a.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

6. Osagie Ize-Iyamu

Shi ma Osagie Ize-Iyamu bai da wuri a majalisar yakin zaben Tinubu duk da kasancewarsa babban ‘dan siyasa kuma malamin addini.

Bayan zamansa a PDP, daga baya ya sauya sheka zuwa APC duk don ya nemi takarar gwamna a Edo, yunkurin da har yau bai yi nasara ba.

7. Dikko Umaru Radda

Kasancewarsa yana gwamna mai-ci bai sa an ga sunan Dikko Umaru Radda a cikin asalin ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba.

An fitar da sunayen kusan lokacin da ake jin kishin-kishin akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan Katsina da hadimin shugaban kasa, Ibrahim Masari.

8. Abba Kabir Yusuf

Abin mamaki ne ganin babu sunan Gwamna Abba Kabir Yusuf a jerin duk da tulin mutane da-dama da fadar shugaban kasa ta zakulo daga Kano.

Watakila za a ce yana cikin kwamitin yakin zabe a jiha, amma dai babu shi a asalin babban kwamitin da The Nation ta ce ya kunshi mutum 223.

Kara karanta wannan

Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu

9. Nuhu Ribadu

Darekta na harkokin mu’amala da masu ruwa tsaki a kamfen APC a zaben da ya wuce bai samu gurbi a tallata takarar da ake yi wannan karo ba.

Ganin kusanci da yake da shi, watakila an ajiye Nuhu Ribadu ne saboda yanayin aikinsa na Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Ribadu
Mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Sauran wadanda ba su cikin kwamitin kamfen APC

10. Timipe Sylva

Saruran wadanda ake kawo wa sun hada da tsohon minista, Timpre Sylva da aka jefa da zargin shirya wa gwamnatin Bola Tinubu juyin mulki.

11. Ahmad Lawan

Bincikenmu ya nuna babu tsohon shugaban majalisar dattawa kuma abokin gwabzawar Tinubu a zaben tsaida gwanin 2023, Sanata Ahmad Lawan.

12. Ben Kalu

Na karshe a jerin namu shi ne Ben Kalu wanda yanzu haka shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma kusa a APC ta reshen Abia.

Majalisar yakin zaben Tinubu ya jawo hayaniya

Kara karanta wannan

Ganin sunan korarriyar minista da mutanen EFCC a kwamitin neman zabe ya jawo surutu

Ganin mutane irinsu Betta Edu, Zacheus Adedeji, da Ngozi Olejeme za su tallata APC ya jawo ce-ce-ku-ce sakamakon yanayin aiki da zargi iri-iri da ake yi masu.

Tsohon Sanata Dino Melaye ya sha alwashin shigar da kara a kotu don kalubalantar nadin Shugaban Hukumar Haraji ta Kasa (NRS), Zack Adedeji a kwamitin.

Dama can Fadar shugaban kasa ta nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, a matsayin Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng