Kwankwaso Ya Kira wa Kansa Ruwa bayan Neman Atiku Ya Hakura da Takara a 2027

Kwankwaso Ya Kira wa Kansa Ruwa bayan Neman Atiku Ya Hakura da Takara a 2027

  • Jigon ADC a Najeriya ya ce Atiku Abubakar ba zai janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 ba, yana kare shekarunsa da lafiyarsa
  • Dan siyasar ya soki kiran da ake yi wa Atiku ya sauka, yana cewa ba shekaru ne kaɗai ke nuna ikon mutum na mulki ba
  • Duk da sabanin ra’ayi, ya ce ADC a shirye yake tattaunawa da jam’iyyun adawa, yana da yakinin za su iya kayar da Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani jigon African Democratic Congress, ADC, Chille Igbawua, ya yi magana kan kiran Atiku Abubakar ya janye daga takara a 2027.

Igbawua ya yi watsi da kiraye-kirayen tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.

ADC ta dura kan Kwankwaso da ya bukaci Atiku ya hakura a takara a 2027
Sanata Rabi'u Kwankwaso da Atiku Abubakar. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Igbawua, tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma mai ba shugaban ADC shawara, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Television.

Kara karanta wannan

An yi wa Kwankwaso wankin babban bargo da ya nemi Atiku ya janye takarar 2027

Jigon ADC ya yi martani ga Kwankwaso

Yayin mayar da martani kan kiraye-kirayen Atiku ya bar takarar ga wani ɗan adawa matashi, Igbawua ya ce:

“Ban san inda ya samo bayanai kan lafiyar Atiku ba.
“Atiku bai canza shekarunsa ba, amma cewa saboda shekarunsa ba zai iya mulki ba, wannan batu ne daban kwata-kwata.
“Na san wasu mutanen da suka ce sun fi Atiku ƙanana, amma ba su da kuzari, basirar tunani da hangen nesan da Atiku yake da su.
“Saboda haka, ba shekarun da aka rubuta a takarda ne abin dubawa ba. Shekaru suna tafiya tare da yanayin lafiya, kuma ban ga wata matsala daga cikin waɗannan a wajen Atiku Abubakar ba.”
An kare Atiku kan kiran sai ya janye daga takara a 2027
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

An zargi an ci mutuncin Atiku

Ya bayyana shawarar cewa Atiku ya janye domin idan adawa ta yi nasara za ta “kula da shi” a matsayin abin zagi da ka iya ƙara raba kan ‘yan adawa.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Ya ce:

“A ce Atiku ya sauka domin idan suka yi nasara za su kula da shi, ta yaya? Wannan cin mutunci ne. Za ku kula da shi ta wace hanya?
“Shin za ku biya masa kuɗin asibiti ne? Ko za ku samar masa da abinci a gidansa?
“Ina ganin wannan rashin ɗaukar nauyi ne matuƙa, a faɗi gaskiya. Wannan batu ya haifar da barna sosai saboda yana ƙirƙirar gibi tsakaninmu.”

Duk da wannan rashin jituwa, Igbawua ya ce ADC a kowane lokaci a shirye take ta tattauna da sauran jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027, cewar Vanguard.

Ya ce:

“A kowane lokaci, muna shirye mu tattauna. Ko tattaunawar za ta yi nasara ko a’a, wannan wani batu ne daban, amma aƙalla tana ba wa ‘yan adawa damar haɗuwa wuri guda.”

Game da yiwuwar jam’iyyun adawa su fito da ‘yan takara da dama domin fuskantar Shugaba Bola Tinubu a 2027, Igbawua ya nuna kwarin gwiwar ADC za ta iya yin nasara.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dawo da zancen zama mataimakin Atiku Abubakar a ADC kafin zabe

Atiku ya bukaci gyara korafinsa kan Tinubu

An ji cewa Atiku Abubakar da ADC sun roƙi Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba su damar gyara ƙarar da suka shigar kan Tinubu da APC.

Dan takarar shugaban kasa a ADC na neman a hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027 bisa zargin gabatar da takardar NYSC ta bogi ga INEC.

Tinubu da APC sun musanta zargin, yayin da kotu ta sanya ranar 28 ga Satumba domin sauraron ƙarar da kuma buƙatar gyaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.