Yanzu Yanzu: Yahaya Bello Ya Janye Goyon Bayansa Ga Bola Tinubu

Yanzu Yanzu: Yahaya Bello Ya Janye Goyon Bayansa Ga Bola Tinubu

  • Akwai alamu da ke nuna cewa gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yanaya Bello ya janye goyon bayansa ga Bola Tinubu
  • An ce gwamnan ya yanke wannan shawarar ne saboda lissafinsa a siyasar Kogi wanda ka iya kawo masa cikas a gaba
  • Wani hadimin gwamnan ya yi watsi da rade-radin, cewa har yanzu ubangidansa na tare da Tinubu

Abuja - Rahoton Nigerian Tribune ya yi hasashen gwamnan jihar Kogi kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Yahaya Bello, ya janye goyon bayansa ga Bola Tinubu.

An nakalto wata majiya a rahoton tana bayyana cewa sabon matsayin gwamnan ya biyo bayan lissafinsa a siyasar jihar ta arewa maso tsakiya gabannin zaben gwamnan Nuwamba.

Tinubu da Bello
Yanzu Yanzu: Yahata Bello Ya Janye Goyon Bayansa Ga Bola Tinubu Hoto: @OfficialAPCng
Asali: Twitter

Majiyar ta bayyana cewa Gwamna Bello ya shiga halin fargaba kan shugabancin Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Zai Iya Kuwa? Bola Tinubu Ya Yi Maganganu Masu Muhimmanci a Jigawa

An tattaro cewa gwamnan na zargin cewa dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikeja a majalisar wakilai kuma sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC na iya shiga tseren neman tikitin gwamnan APC a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Feleke dan hannun damar Tinubu ne kuma shine abokin tafiyar dan takarar gwamnan APC a zaben Nuwamban 2015, Abubakar Audu, wanda ya rasu jim kadan bayan kada kuri'arsa.

Hadimin Bello ya gargadi gwamnan Kogi da ya janye goyon bayansa ga Tinubu

An tattaro cewa an gargadi gwamna Bello wanda shine jagoran matasa na kwamitin yakin neman zaben Tinubu-Shettima, a kan cewa goyon bayan Tinubu na iya haifar da gwamnatin Faleke a jihar.

Tsoron na kusa da Bello shine cewa Tinubu zai zamo da wuka da nama kan matsayin da kowa zai samu a jam'iyyar idan ya lashe zaben shugaban kasa, inda zai bar ubangidansu a cikin duhu, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

Wani jigon jam'iyyar a jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce Bello baya goyon bayan mika mulki zuwa yankin Kogi ta yamma inda daga nan ne Faleke ya fito.

An kuma tattaro cewa gwamnan ya rigada ya nuna goyon bayan Akanta Janar a jihar, Jubril Mommoh wanda ya fito daga Kogi ta gabas.

Ya ce:

"Gwamnan na son makusancinsa, wanda zai iya rufe abubuwan da ya aikata a matsayin magajinsa.
"Don haka yana taka-tsantsan da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa. Ya san cewa Tinubu zai duba yadda ya yi nasara da goyon bayan gwamnonin arewa kuma zai iya la'akari da Kogi ta yamma da Faleke."

Ubangidana na tare da Tinubu, In ji Fanwo

Da yake martani, Kingsley Fanwo, kwamishinan labarai na jihar Kogi, ya ce rade-radin da ake yi kan gwamna Bello game da dan takarar shugaban kasa na APC kanzon kurege ne.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Wamakko, Ministan Buhari da Sauran Mambobin Kamfen Din APC a Sokoto

"Gwamna Yahaya Bello ya kasance shugaba mai fuskantar inda ya sanya gaba da magana daya wanda ke da karfin gwiwar tsayawa tsayin daka a kan zabinsa."

Daraktar yakin neman zaben Tinubu ta fice daga APC

A wani labari makamancin wannan, jaridar Punch ta rahoto cewa Naja’atu Muhammad, darakta a kwamitin yakin neman zaben Tinubu ta yi murabus.

Ta kasance daraktar jama'a a kwamitin kamfen din APC kuma ta yi murabus ne ana saura wata daya zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel