Gwamnan APC yace ba zai bari APC taci zabe a jiharsa ba a 2019

Gwamnan APC yace ba zai bari APC taci zabe a jiharsa ba a 2019

- Gwamnan jihar Ogun yayi alkawarin kin goyon bayan Dan takarar gwamnan jiha

- Ya tabbatar da cewa zai yi duk abinda yakamata don ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce

- Gwamna yace ba zai bar jam'iyyar ba, sai ya nemi takarar kujerar sanatan jihar na tsakiya

Gwamnan APC yace ba zai bari APC taci zabe a jiharsa ba a 2019

Gwamnan APC yace ba zai bari APC taci zabe a jiharsa ba a 2019
Source: Facebook

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, yayi alkawarin kin bada goyon bayan shi ga Dan takarar shugabancin gwamnan jihar.

Mista Amosun makusanci ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi alkawarin aiki tukuru don ganin zarcewar shugabancin shugaban kasar.

Yace ba zai bar jam'iyyar APC ba kuma zai nemi kujerar sanatan jihar ta tsakiya a karkashin inuwar jam'iyyar.

Mista Amosun yayi maganar ne a ranar Monday a garin Abeokuta yayin da sukayi taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC wanda ya samu halartar Dan takarar gwamnan da yake so na jam'iyyar APM, Adekunle Akintunde.

DUBA WANNAN: Yawan kungiyoyin da suka bar Buhari don Atiku

Sanarwar gwamnan ta biyo bayan barin yan jam'iyyar APC 26 magoya bayan shi zuwa jam'iyyar APM.

Mista Amosun yace ya yi iya bakin kokarin shi wajen ganin Mista Akinlade da sauran yan jam'iyyar da sukayi fushi basu bar APC ba.

Yayi alkawarin yin duk abinda zai iya wajen ganin nasarar Mista Akinlade da sauran masu fushin a sabuwar jam'iyyar su.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel