Ganin Sunan Korarriyar Minista da Mutanen EFCC a Kwamitin Neman Zabe Ya Jawo Surutu
- Mutane da dama sun nuna mamakin ganin sunan tsohuwar ministar yaki da talauci cikin masu yi wa APC kamfen
- Masu sukar lamirin sun gano cewa matakin na iya gurgunta amincin al'umma ga gwamnatin Bola Tinubu
- A matsayinsa na shugaban NRS, an soki yadda APC ta sa Zacheus Adedeji a kwamitin yakin neman zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ganin sunayen wasu mutane cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ya soma jawo abin magana a wurare.
A cikin mutanen da za su jagoranci tallata Bola Ahmed Tinubu akwai wadanda wasu ke ganin bai kamata a ga sunayensu ba.

Source: Getty Images
Betta Edu za ta taya Bola Tinubu kamfe
Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya nuna yadda ake tir da ganin an jawo irinsu Betta Edu wadanda aka kora daga ofis.
Beta Edu wanda ta rasa kujerarta ta minista tun a 2024 ita ce darektar da za ta jagoranci jawo mata cikin tafiyar Bola Tinubu.
A farkon 2024 Mai girma shugaban kasa ya dakatar da ita saboda zargin ta bada umarni a tura N585m cikin wani asusun banki.
Edu ta rika sintiri a ofishin hukumar EFCC lokacin binciken kuma ta rasa kujerarta, har aka canza ta da Farfesa Nentawe Yilwatda.
Za a yi shari'a da Tinubu kan nadin Adedeji
Shi kuwa Zack Adedeji zai taya jam’iyyar APC nemo kudi a kwamitin kamfe, Jaridar People Gazette ta ce hakan ya tada kura sosai.
Abin da ya sa nadin na shi ya jawo surutu shi ne ganin hukumar tattara haraji ta kasa tana hannun shi tun a Satumban 2023.
Saboda haka tsohon Sanata daga jihar Kogi, Dino Melaye ya sha alwashin zai yi kara a kotu domin kalubalantar lamarin.

Kara karanta wannan
Duk da suna jam'iyya 1, Gwamna Radda ya yi maganar nadin da Tinubu ya yi maaa a kwamitin kamfen
Sanata Dino Melaye wanda shi kan shi lauya ne, ya yi magana a Facebook yana cewa akwai cin karo da juna wajen nadin.
Ya ce bai kamata jami’in gwamnati da ake biya albashi daga lalitar al’umma ya tafi goyon bayan ‘dan takaran siyasa a zabe ba.
Alamar tambaya game da Ngozi Olejeme
Haka zalika akwai Ngozi Olejeme wanda ake shari’a da ita bayan kujerar da ta rike na shugabaar hukumar NSITF a shekarun baya.
Wajen yakin zaben Tinubu/Shettima a jam’iyyar APC, Darektar tsare-tsaren zamani a Kudu maso kudu ita ce Ngozi Olejeme.
A shekarar da ta wuce ka gurfanar da Olejeme a babbar kotun tarayya a Abuja, ana zarginta da wanke kudi har N1bn na haram.
Tun tuni ake gayyatar ta zuwa ofishin EFCC domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kudin NSITF daga 2014 zuwa 2015.
Ban da tuhumar satar N69bn da ake yi mata, a shekarar 2020 aka ji alkali ta bada umarnin karbe wasu kadarori 48 da ta mallaka.
Dino Melaye ya wallafa bidiyo cewa zai je kotu
An fitar da kwamitin yakin zaben Tinubu
An ji labarin nada kwamitin da zai yi wa Bola Tinubu kamfe, tsohon gwamnan Zamfara wato Abdulaziz Yari ya zama Darekta Janar .
Ranar Asabar, Fadar shugaban kasa ta fitar da sunayen duka jami'an da za su jagoranci tafiyar yakin neman zaben shugaban kasa a 2027.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, shi ne zai kasance sakataren kwamitin, yayin da Tinubu da Kashim Shettima su ke shugabanni.
Asali: Legit.ng

