Baki Ke Yanka Wuya: Fadar Shugaban Kasa Ta Kalubalanci Peter Obi kan Zaben 2027
- Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Peter Obi kan ikirarinsa cewa ya bar Anambra ba tare da basussuka ba bayan ya kammala wa’adinsa a 2014
- Bayo Onanuga ya ce gwamnatin Anambra ta gabatar da bayanan kuɗi da ke nuna akwai wasu basussuka da gwamnatin Obi ta bari
- Obi ya ce ya biya sama da N35bn na tsofaffin bashin alawus da hakkokin ma’aikata, kuma ya ƙalubalanci duk mai hujjar akasin haka ya gabatar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta tsoma baki kan batun basussukan da Peter Obi ya bari bayan kammala wa'adin mulkinsa a jihar Anambra.
Fadar ta ƙalubalanci Obi da ya cika alkawarinsa na daina yaƙin neman zaɓe idan aka tabbatar da cewa ya bar basussuka bayan ya bar mulki.

Source: Facebook
Onanuga ya ce Obi ne ya kafa sharadin

Kara karanta wannan
Ba kamar Tinubu ba, Peter Obi ya yi ta maza da aka nemi a saki takardun karatunsa
Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026.
Ya ce Obi da kansa ne ya kafa wannan sharadi bayan ya yi alkawarin daina yaƙin neman zaɓen idan aka tabbatar da cewa ya bar bashi.
Onanuga ya ce Obi ya taɓa ikirarin cewa ya bar Anambra cikin cikakken tsari ba tare da bashin gwamnati ba, har ma ya ce zai janye daga takarar shugaban ƙasa idan aka tabbatar da akasin haka.
Fadar ta ce gwamnatin Anambra ta gabatar da hujjoji
Onanuga ya ce gwamnatin Anambra ta gabatar da bayanan kuɗi da suka saɓa wa bayanin tsohon gwamnan.
A cewarsa, bayanan sun nuna cewa gwamnatin Obi ta bar wasu basussuka da suka shafi ma’aikatan hukumar samar da ruwa, malamai da kuma hakkokin fansho da kuɗaɗen sallama.
Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin ta karɓi wasu basussuka domin ayyukan da ya bayyana a matsayin marasa muhimmanci.
“Yanzu komai ya koma hannunsa. Shin zai cika barazanar da ya yi ta hanyar janye wa daga takarar?” Onanuga ya tambaya.
Obi ya musanta barin basussukan ma’aikata
Ce-ce-ku-ce ɗin ya biyo bayan sabon bayani da Peter Obi ya yi kan shekaru takwas da ya yi yana mulkin Anambra.
Tsohon gwamnan ya ƙaryata zargin cewa ya bar bashin albashi, fansho, kuɗaɗen sallama da kuma bashin ’yan kwangila.
Obi ya ce gwamnatinsa ta biya sama da N35 biliyan na tsoffin kuɗaɗen sallama da basussukan da aka gada.
Ya kuma dage cewa lokacin da ya bar mulki babu wani bashin albashi, fansho ko kuɗin sallama da ake bin gwamnati.
Obi ya ƙalubalanci duk wanda ke da hujjar akasin abin da ya faɗa da ya gabatar da ita.
“Idan wani zai iya tabbatar da wani abu da ya saɓa da wannan, zan daina yaƙin neman zaɓe,” in ji shi.

Source: Twitter
Fayose ya yi hasashen nasarar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi hasashen nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Ayo Fayose ce yana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai samu sama da ƙuri’u miliyan 12 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng
