Yanzu-yanzu: Shugaban kamfen ɗin Atiku, Gbenga Daniel, ya fice daga PDP ya koma APC
- Otunba Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun kuma shugaban tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar ya koma APC
- Tsohon gwamnan ya sanar da komawarsa cikin gaggawa inda ya ce goyon bayan da ya ke bawa gwamnan jiharsa Dapo Abiodun na dalilin da yasa ya koma APC
- Daniel ya nemi afuwar tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP inda ya ce abin ya zo masa cikin gaggawa ne shi yasa bai ankarar da su da wuri ba
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya koma jam'iyyar All Progressive Congress, APC mai mulki, Vanguard ta ruwaito.
Gbenga jigo ne a babban jam'iyyar hamayya ta PDP kuma shine ya jagoranci yakin neman zaben shugabancin kasa na Atiku Abubakar.
DUBA WANNAN: Dan Nijar ne ba bahaushe ba ya kashe bayarabe a Shasha, in ji shaidar gani da ido
Ana sa ran Daniel zai tafi ya karbi katin jam'iyarsa na APC kafin a rufe yin rajistan sabbin yan jam'iyyar a yau Talata.
A cikin sanarwar da ya fitar, Daniel ya nemi afuwar tsohuwar jam'iyyarsa saboda rashin sanar da su da wuri, inda ya ce goyon bayan gwamnan jiharsa ta Ogun, Dapo Abiodun na daga cikin dalilan da yasa ya dauki matakin.
Ya yi bayanin cewa ya dauki matakin gaggawar ne saboda bukatar da shugaban riko na APC na kasa ya yi na cewa zai ziyarce shi tare da gwamnoni uku.
"Ina ganin ya dace in sanar da gidan kafin labarin ya bazu," in ji shi.
KU KARANTA: Allah ya yi wa Sanata Etang Umoyo rasuwa
Wata majiya na kusa da tsohon gwamnan na Ogun ta ce zai gana da shugaban kwamitin rikon kwaryan na APC gwamna Mai Mala Buni a ranar Laraba.
Ana sa ran gwamnoni suku za su halarci taron, gwamnonin sun hada da Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Badaru Abubakar na jihar Jigawa.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng