Rikicin Dikko Radda da Hadimin Tinubu Ya Farraka Jam’iyyar APC a Katsina
- An tsare jami'an tsaron gwamnan Katsina sakamakon zargin rushe allon tallar zaben Shugaba Bola Tinubu
- Ana ganin rigimar na da nasaba da takaddamar da ke tsakanin bangaren Ibrahim Masari da na Dikko Umru Radda
- Yayin da majiyoyi ke tabbatar da cewa an tsare jami'an, ita kuma rundunar ‘yan sanda ta ce gayyatarsu kawai aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Sabanin da ke tsakanin Dikko Umaru Radda da hadimin Shugaban kasa, Ibrahim Kabir Masari yana illata APC.
An samu rashin jituwa tsakanin manyan ‘yan APC - Gwamnan Katsina da Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa.

Source: Facebook
An tsare dogaran Gwamnan Katsina a Abuja
Rahoton Daily Trust ya nuna lamarin har ya kai an tsare dogarin Gwamnan Katsina, SP Abdulganiyu Bello da kuma jami’in CSO.
CSO shi ne babban jami’in tsaro da ke tare da gwamna. Yanzu haka DSP Hassan Bello yana can hedikwatar ‘yan sanda a Abuja.
An kira dogarin tare da babban jami’in tsaron zuwa Abuja domin su amsa tambayoyi game da rusa fastocin Bola Tinubu a Katsina.
Rusa fastocin APC ya jefa Gwamnan Katsina a matsala
Game da fastocin da aka rusa a kusa da gidan gwamnati, mutane sun ce an sa hotunan shugaban kasa amma an yi watsi da na gwamna.
An yi amfani manyan hotunan shugaban kasa da na Ibrahim Masari, amma an ce sai aka sa karamin hoton Mai girma gwamna a can gefe.
'Yan sanda sun ce ba su tsare dogaran gwamna ba
Amma da aka yi magana da Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Anietie Iniedu, ya ce ba tsare wadannan jami’an tsaro aka yi ba.
CSP Anietie Iniedu ya ce an kira su ne kawai domin ‘yan sanda su yi masu tambayoyi. Sai dai ana cewa har yau ba a kara ganinsu ba.
Leadership ta ce kakakin ya karyata cewa Abdulganiyu Bello da Hassan Bello suna hannunsu tun ranar 20 ga watan Agusta 2026.
Yunkurin da Gwamnatin Katsina take yi

Kara karanta wannan
Ganin sunan korarriyar minista da mutanen EFCC a kwamitin neman zabe ya jawo surutu
Wannan abin bai yi wa ‘yan APC a Katsina dadi ba musamman bayan ganin babu sunan gwamna a kwamitin zaben shugaban kasa.
An ce Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Katsina, Abdulkadir Mamman Nasir ya je Abuja domin ganin an saki wadannan jami’ai.
Bayanai sun kuma zo cewa an yi ram da wani ‘dan siyasa Aminu Sanda bisa zargin cewa yana da hannu a kan abubuwan da suka faru.
Sabani tsakanin mutanen Radda da na Masari
Wannan ya fito da rashin jituwa da ke tsakanin shugabannin APC na reshen Katsina da manyan jam’iyyar ‘yan asalin jihar da ke Abuja.
An dade ana cewa Gwamna Radda yana kuka da yadda ‘yan Abuja ke kawo masa cikas.
Wannan ya kara tabbata lokacin da aka tsige Ahmed Musa Dangiwa daga matsayin minista, aka canza shi da Mutaqqa Rabe Darma.

Source: Facebook
Dangiwa ya yi aiki da Radda a matsayin sakataren gwamnati yayin da ake cewa Muttaqa Rabe Darma suna bangaren Ibrahim Masari.
Maiwada Danmallam wanda hadimin gwamnan Katsina ne, ya musanta cewa akwai rashin jituwa tsakanin Radda da su Alhaji Masari.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Gwamnan Katsina bai cikin kwamitin tallata Tinubu
Rashin ganin sunan Gwamnan Katsina da wasu ya sa za a sake duba kwamitin kamfen APC, duk an ce jam'iyyar ta karyata wannan labari.
Ana jita-jita cewa Fadar shugaban kasa ta janye jerin mambobin kwamitin yakin neman zaben 2027 domin sake yin gyara saboda kura-kurai a ciki.
Baya ga manta wa da wasu gwamnoni da aka yi, jerin ya kuma kunshi wasu mutanen da suke wasan buya da jami'an hukumar EFCC a Najeriya.
Asali: Legit.ng
