Ba Haka Aka So ba: Saudiyya Ta Ki Amincewa da Bukatar Najeriya kan Aikin Hajjin 2027

Ba Haka Aka So ba: Saudiyya Ta Ki Amincewa da Bukatar Najeriya kan Aikin Hajjin 2027

  • Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya ta gabatar mata kan aikin Hajjin shekarar 2027 mai zuwa
  • Najeriya za ta samu gurbi 50,000, wanda ya haɗa da 35,000 na mahajjatan da suka fito daga bangaren gwamnati da 15,000 na kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi
  • NAHCON ta ce wa’adin dora bayanan masu shirin zuwa Hajjin 2027 ya kasance 26 ga Satumba, 2026, kuma ba za a ƙara lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da cewa Masarautar Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya ta ƙara yawan guraben da aka ware wa ƙasar domin aikin Hajjin 2027.

Hakan na nufin adadin guraben Najeriya zai ci gaba da kasancewa yadda yake, duk da ƙarin yawan Musulman da ke son zuwa aikin Hajji daga sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

Saudiyya ta ki amincewa da bukatar Najeriya
Shugaban hukumar NAHCON, Ismail Abba Yusuf Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar NAHCON ta sanya a shafinta na X a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026.

Najeriya ta nemi karin gurabe

NAHCON ta ce ta tattauna da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin neman ƙarin guraben mahajjata.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne saboda ƙarin yawan ’yan Najeriya da ke son gudanar da ibadar Hajji, da kuma buƙatun da wasu hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi suka gabatar na neman ƙarin gurabe.

Sai dai hukumomin Saudiyya sun sanar da Najeriya cewa ba za su iya ƙara guraben ba.

Saudiyya ta bayyana dalilanta

A cewar NAHCON, Saudiyya ta danganta matakin da ƙarancin damar ɗaukar ƙarin mutane, matsalolin tsare-tsare da tsarin gudanarwa a wuraren ibadar Hajji.

Hukumomin Saudiyya sun kuma bayyana cewa manufofinsu na yanzu na buƙatar a bi ƙa’idojin adadin mahajjatan da aka amince da su ga kowace ƙasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

Saboda haka, Najeriya za ta ci gaba da samun jimillar gurabe 50,000 a aikin Hajjin 2027.

Daga cikin adadin, gurabe 35,000 ne aka ware wa mahajjatan da gwamnati ke kula da su, yayin da 15,000 aka ware wa kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi.

NAHCON ta ce ta fahimci damuwar mahajjata

Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya ce hukumar ta fahimci takaicin da wannan mataki zai iya haifarwa ga masu shirin zuwa Hajji da hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi.

Ya ce hukumar ta yi amfani da duk hanyoyin diflomasiyya da na gudanarwa da suke akwai wajen neman ƙarin gurabe, amma ta mutunta matsayar ƙarshe da hukumomin Saudiyya suka yanke.

Ambasada Yusuf ya ce suna fahimtar babban burin Musulman Najeriya na gudanar da aikin Hajji da kuma tsammanin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki na samun ƙarin gurabe.

Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin neman ƙarin kason, Saudiyya ta sanar da matsayarta na ƙarshe bisa la’akari da yanayin gudanar da aikin da kuma iyakar wuraren ibadar.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Dattawa daga Arewa sun aika sako ga Tinubu bayan fetur ya kai N1500

Saudiyya ta ki kara guraben aikin hajji ga yan Najeriya
Shugaban NAHCON, Ismail Abba Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Source: Facebook

Kamfanonin da za su yi jigila a Hajjin 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar mahajjata a 2027.

NAHCON ta amince da kamfanonin jiragen sama guda biyar domin gudanar da jigilar mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng