Ana tsaka da Musayar Wuta, Manyan Shugabannin Kasar Iran Za Su Shiga Amurka
- Amurka za ta bar wata tawagar Iran, ciki har da Shugaba Masoud Pezeshkian, shiga birnin New York domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya
- Matakin na zuwa ne duk da yakin da Amurka da jamhuriyar musulunci ta Iran ke yi wanda ya shiga wata na bakwai
- Tawagar Iran za ta kasance ƙarama fiye da ta bara kuma za a sanya mata takunkumin zirga-zirga da sayen wasu kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington — Amurka za ta bai wa wata tawagar Iran damar halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a brinin New York a mako mai zuwa.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba, 2026.

Source: Getty Images
Vanguard ta ruwaito Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar da cewa matakin zai shafi Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

Kara karanta wannan
Mutuwa ta girgiza ɗan takarar gwamna, mutum 6 daga cikin mutanensa sun rasu lokaci 1
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce,
“Dangane da wajibcinmu na ƙasa mai masaukin baki, za a bai wa babbar tawagar gwamnatin Iran damar halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya.”
Sai dai jami’in ya ƙara da cewa tawagar za ta kasance karama idan aka kwatanta da ta bara. Haka kuma, za a sanya mata takunkumin zirga-zirga tare da hana sayen kayayyakin alatu da wasu kayayyaki.
Yakin Amurka da kasar Iran
Hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran tun ƙarshen watan Fabrairu ne suka haddasa yakin da ya bazu zuwa sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar toshe mashigar tekun Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi, lamarin da ya sa farashin man fetur a duniya ya yi tashin gwauron zabi.
A cikin makonnin baya-bayan nan, an sake samun ƙaruwa a fadan da ke tsakanin Amurka da Iran, yayin da jigilar kayayyaki ta ci gaba da fuskantar takura a mashigar Hormuz da mashigar Bab al-Mandab da ke gabar tekun Yemen.
Amurka ta hana Abbas shiga
Matakin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da Washington ta tabbatar da cewa ta hana Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas samun takardar izinin shiga Amurka domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya.
Wata majiya ta tabbatar da hakan ranar Laraba, inda ta ce wannan ne karo na biyu a jere da Amurka ta ɗauki irin wannan mataki.

Source: Twitter
Matakin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ɗauka a bara ya tilasta wa shugaban Falasɗinun, wanda ke yawan halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, yin jawabi ga shugabannin duniya ta bidiyo.
A cikin wata sanarwa da ba ta ambaci Abbas da sunansa ba, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce za ta hana bayar da biza ga mambobin Kungiyar 'Yantar da Falasɗinu (PLO) da jami’an Hukumar Falasɗinawa.
Sanarwar ta ce hakan ya faru ne saboda “gazawarsu wajen yin gyare-gyare, sabanin alkawuran da suka ɗauka wa Amurka, da kuma ci gaba da ayyukan da ke lalata damar samun zaman lafiya.”
Iran ta harbo jiragen yakin Amurka
Kun ji cewa sakarun sojojin Iran sun harbo aƙalla jiragen sama marasa matuƙi na Amurka kirar MQ-1 guda biyu a ’yan kwanakin nan.
Jiragen Predator da Gray Eagle na daga cikin nau’ikan MQ-1 da sojojin Amurka ke amfani da su wajen sa ido, kuma suna iya ɗaukar makamai masu linzami.
Asali: Legit.ng

