Zaben Shugaban kasan Najeriya
Mallam Jabir Ibrahim Yaro ya musanta kasancewarsa cikin kwamitin yakin neman zaben mutum 59, yana cewa ba a tuntube shi ba kuma bai amince da saka sunansa ba.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC watanni uku bayan ya fice daga ADC bisa zargin an yi magudi a zaɓen fidda gwani.
Seyi Makinde da APM sun kai Gwamnan Abia Alex Otti kotu kan kuɗin N200m da ake buƙata daga masu neman shugaban ƙasa domin tallan yaƙin neman zaɓe.
Rigima mai tsanani ta barke tsakanin tafiyar 'OK Movement' da NDC kan tsarin tafiyar da yakin zabe, ya haddasa rabuwar kai a kawancen Peter Obi da Rbiu Kwankwaso.
Wani hadimin ‘dan takaran shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta maido tallafin fetur amma a cire daga an yi zabe.
Za a ji yadda tsofaffin shugabannin majalisun jihohi na Najeriya (FOPSHAN) suka nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu don ya zarce a kan mulki a 2027.
Dan takarar shugaban ƙasa na AAC, Omoyele Sowore, ya ce ba zai amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa idan ya zama shugaban Najeriya a zaben 2027.
Shehu Sani ya ce ya kamata fafatawar 2027 ta kasance tsakanin Bola Tinubu, Peter Obi, Sowore, Makinde, Adebayo, Duke da sauran ’yan takarar da suka fito daga Kudu.
Ganin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na shirin neman kujerar shugaban ƙasa da mataimakinsa, jam'iyyar NDC ta fitar da kwamitin yakin neman zaben 2027.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari