Surutun Jama’a da Mantawa da Wasu Ya Jawo An Janye Sunayen Kwamitin Kamfen Tinubu

Surutun Jama’a da Mantawa da Wasu Ya Jawo An Janye Sunayen Kwamitin Kamfen Tinubu

  • Matsaloli kamar cire sunayen jiga-jigai sun haifar da matsala bayan fitar da kwamitin yakin neman zaben APC
  • An kuma sanya sunayen wadanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa, hakan ya kawo tarnaki ga shirin takarar
  • Ko da an yi garambawul, tsohon gwamna Abdulaziz Yari ne dai zai jagoranci kwamitin a matsayin Darakta Janar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Da alama an tursasa Fadar shugaban kasa game da kwamitin yakin zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima da aka fitar.

A halin yanzu an janye sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na APC da nufin a yi wasu ‘yan kananan kwaskwarima.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima ana kamfe a 2023 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Za a sake duba sunayen 'yan majalisar kamfen APC

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ya zama dole saboda korafi da maganganu da aka rika samu daga ciki da wajen jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Ganin sunan korarriyar minista da mutanen EFCC a kwamitin neman zabe ya jawo surutu

Akwai manyan ‘yan APC da ya kamata a ga sunayensu amma babu su, sannan akwai wadanda kawo su ciki ya zama abin magana.

Wata majiya ta shaida cewa an yi maza an janye sunayen da nufin a yi wa jerin garambawul domin rufe bakin ‘yan hamayya a Najeriya.

An ji yadda kwamitin ya kunshi wasu da ke da tabo a jikinsu, duk da zarge-zargen da ake yi masu, za su yi aikin yakin neman zaben 2027.

Babu maganar rantsar da kwamitin kamfe tukuna

Zuwa yanzu ba a sanar da lokacin rantsar da ‘yan kwamitin kamfen ba, an jinkirta ne domin akwai bukatar a sake yin aiki a kan batun.

Bayanan da jaridar ta samu ya ce ba za a canza Darekta janar ko sakataren kwamitin kamfen ba, canjin a cikin sauran ‘yan kwamiti ne.

Aminiya ta ce abin da ya kara jan hankali shi ne ganin sunayen wadanda ake zargi da rashin gaskiya da kuma wasu manya da aka manta da su.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

APC ta manta da wasu cikin majalisar yakin zabe

Akwai kuma wasu ‘yan siyasar da tuntube ya jawo ba a ga sunansu a cikin majalisar ba.

Baya ga haka, akwai wadanda ake ganin cewa kuskure ne ganin su cikin harkar yakin neman zabe saboda mukaman da suke rikewa.

An zabi Zacheus Adedeji ya zama mataimakin shugaban darektan kwamitin nemo kudi alhali shi yake rike da hukumar haraji ta kasa.

Legit Hausa ta lura da surutun da ake yi a kwamitin da aka bukaci ya lura da harkar tattara bayanai karkashin jagorancin Bisoye Coker.

Ban da cewa Dr. Coker tana kan kujerar gwamnati da ba ta dace da siyasa ba, an sa tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar a kasan ta.

Kamfen APC
Dandazon magoya bayan APC lokacin kamfen Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sunayen manyan APC da ba su cikin 'yan kamfe

An manta da Ministan jirage kuma kakakin kamfen APC a 2023, Festus Keyamo da shugaban yakin zabe lokacin, Sanata Simon Lalong.

Haka kuma kwamitin bai kunshi sunayen manyan jam’iyya irinsu Yahaya Bello, Gbenga Daniel, Ibikunle Amosun da Rt. Hon.Ben Kalu ba.

Kara karanta wannan

Duk da suna jam'iyya 1, Gwamna Radda ya yi maganar nadin da Tinubu ya yi maaa a kwamitin kamfen

Wani abin mamaki shi ne rashin ganin sunan Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda wanda yake rike da jihar tsohon shugaban kasa.

Nadin kwamitin kamfe zai kare a kotu

Kun ji cewa nadin mutane akalla uku ya jawo raddi da maganganu marasa dadi a kan kwamitin tallata Bola Tinubu/Kashim Shettima.

Shigar da sunayen mutane irin su tsohuwar minista Betta Edu da sauran wadanda EFCC ke bincike a kwamitin zai iya zama matsala.

Tsohon Sanata Dino Melaye ya bayyana aniyarsa ta kalubalantar wadannan nadin a kotu domin kare amincin tsarin gwamnati a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng