An Kai Karar Babban Malamin Musulunci a Kano gaban Kotu kan Zargin Batanci ga Annabi SAW

An Kai Karar Babban Malamin Musulunci a Kano gaban Kotu kan Zargin Batanci ga Annabi SAW

  • Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a Kano ta fara sauraron ƙarar da wasu ƙungiyoyin Musulunci suka shigar kan malamin Sheikh Lawan Abubakar Triumph
  • Ƙungiyoyin sun zargi malamin da yin kalaman batanci ga Annabi SAW, inda lauyansu ya nemi a tura ƙarar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Kano
  • Kotu ta ƙi bayar da umarnin rufe masallacin da Malam Lawan ke jagoranta, tana mai cewa ba ta da ikon yin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a ƙaramar hukumar birnin Kano ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan babban malamin musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Triumph.

Wasu ƙungiyoyin Musulunci ne suka shigar karar kan malamin addini Lawan Abubakar Triumph bisa zargin yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

Triumph.
Babban malamin addinin musulunci a Kano, Sheikh Lawan Abubakar Triumph Hoto: Sheikh Lawan Abubakar Triumph
Source: Facebook

Kotu ta yi zama kan Sheikh Triumph

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun shari'ar musulunci ta samu zama kan wannan shari'a a yau Alhamis, 17 ga watan Satumba, 2026.

Lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Hajj, ya shaida wa kotun da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta cewa sun shigar da ƙarar kai tsaye kan wanda ake ƙara.

Ya buƙaci kotun ta tura ƙarar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano domin gudanar da cikakken bincike kan zargin da suke wa Malam Lawan Triumph.

Lauyan malamin ya nemi karin lokaci

Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Barista Abdurrazak A. Ahmad, ya nemi a ba shi lokaci domin nazarin zarge-zargen da ake yi wa wanda yake karewa tare da mayar da martani a kansu.

Lauyan malamin ya kuma ƙalubalanci ikon kotun na sauraron ƙarar, yana mai musun cewa ba ta hurumin karbar wannan shari'a.

Barista Ibrahim Umar ne ya jagoranci tawagar lauyoyin da ke kare Sheikh Lawan Triumph a gaban kotun da ke zama a kofar Kudu, yankin karamar hukumar kwaryar birnin Kano.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

Kotu ta ƙi rufe masallaci Triump

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar masu kara na ta bayar da umarnin rufe masallacin da Malam Lawan ke jagoranta.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce kotun ba ta da ikon bayar da irin wannan umarni na rufe masallaci.

Kotun sharia.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita da alamar nuna kotun shari'a Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron batun zuwa ranar 24 ga Satumba 2026, domin bayyana matsayinta kan ƙarar, kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito.

Malam Triumph ya yi zama da Shura

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Lawan Abubakar Shua’ibu Triumph ya bayyana sakamakon ganawarsa da Shura a Kano bayan zarge-zargen da aka yi masa.

Malamin addinin Islama ya bayyana cewa an gabatar masa da tambayoyi masu zurfi sosai, inda ya gabatar da hujjoji daga littattafan da suka dace kan zargin da ake masa na taba mutuncin Annabi S.A.W.

Sheikh Triumph ya bayyana cewa majalisar Shura ta Kano ta nuna gamsuwa da bayanan da ya gabatar, sai dai ta ba shi shawarar ya tausasa harshe a lokacin da yake wa’azi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262