Tinubu Ya Gamu da Matsala har a Majalisa daga Nadin Kwamitin Yakin Neman Zabe
- Wasu ‘yan Majalisar wakilai sun ce bai dace a cusa shugabannin Ma'aikatar Tsaro a cikin kwamitin yakin zaben siyasa ba
- Shigar da shugaban hukumar haraji a majalisar kamfe ya sa ana tsoron yin amfani da kudin haraji wajen yakin zaben APC
- 'Yan kungiyar SDG a Majalisar tarayya sun jaddada cewa dole ne a raba tsakanin aikin ofis da tallata takarar Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wasu ‘yan majalisa da ke karkashin kungiyar Save Democracy Group (SDG) sun soki kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu.
‘Yan majalisar wakilan tarayya sun ce cusa wasu jami’an gwamnati zai kawo cin karo tsakanin nauyin da yake kansu da kuma harkar siyasa.

Source: Getty Images
Kungiyar ta ce duk da mutane suna da damar shiga siyasa, amma ya zama dole a kare hukumomin gwamnati daga harkar a cewar This Day.
An ji kungiyar ‘yan majalisar ta fitar da jawabi da sa hannun shugabanta, Awaji-Inombek Abiante, da kuma Abubakar Kusada da Mansur Jega.
Me ya kai Ministocin tsaro cikin kamfe?
Wadannan ‘yan majalisa da suka fito daga APC, NDC da ADC sun soki yadda aka sa Christopher Musa da Bello Matawalle a kwamitin kamfe.
Suka ce a matsayinsu na Ministocin tsaro, babu abin da ya hada wadannan jami'ai da kwamitin tallata takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima.
‘Yan majalisar suka ce ofishinsu yana kula da harkokin tsaro ne da sha’anin sojoji kuma bai kamata a zargi sojoji da shiga siyasar jam’iyya ba.
Suna ganin hakan zai iya jawo mutane su daina ganin jami’an tsaro za su zama masu adalci domin kuwa sojoji ba na wata jam’iyya ba ne.
An bukaci ministocin su maida hankali a kan aikinsu musamman da ake fama da matsalolin tsaro.
Zargin amfani da haraji wajen yakin zabe Fry

Kara karanta wannan
Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu
Haka zalika an soki yadda aka ga Shugaban hukumar haraji ya samu gurbi a majalisar kamfe, aka sa shi a kwamitin nemo wa APC kudi.
Premium Times ta rahoto cewa a nan ma sun ce wannan zai ka ga zargin hukumar gwamnati da taimaka wa jam’iyyar APC ta ci zabe.
Ba su tsaya a nan ba, sun yi tir da yadda aka ba Shugaban ofishin kasafin kudi matsayin ma’aji na kwamitin yakin neman takarar 2027.

Source: Getty Images
SDG ta ce dole Tanimu Yakubu da ofishin kasafin kudi su guji yin abin da zai bata kimarsu har ta kai a zarge su da nuna son kai wajen aiki.
An yi kira ga masu rike kujerun gwamnati da aka ba kujera a majalisar kamfe su janye jikinsu, su hakura da cakuda siyasa da aikin ofishinsu.
Kan APC ya rabu a jihar Katsina
Ana zargin cewa rigima ta danno APC a Katsina bayan damke dogaran Gwamna Dikko Radda saboda an lalata allon Bola Tinunu.
An kama dogaran Gwamnan Katsina sakamakon zarginsu da hannu cikin lalata allunan tallar Bola Tinubu da Ibrahim Kabir Masari.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
Wannan sabani tsakanin Dikko Umaru Radda da Ibrahim Kabir Masari ya raba kan APC a lokacin da aka soma yakin neman zaben 2027.
Asali: Legit.ng
