Kwankwaso da Obi Sun Zo da Wani Tsari da Zai Iya Zama Matsala ga Tinubu a Zaben 2027
- Jigo a jam’iyyar PDP, Injiniya Anselm Ijebor, ya ce tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a NDC zai sauya lissafin siyasar Najeriya
- Ijebor ya ce takarar Obi ta gabatar da sabon zaɓi na mussmman a fafutukar neman shugabancin Najeriya a 2027
- Ya ce kasancewar Obi da Kwankwaso a takardar zaɓe zai ba masu kaɗa ƙuri’a wata kafa ta daban da za su yi la’akari da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Injiniya Anselm Ijebor, ya ce tikitin takarar shugaban kasa na NDC da ya hada Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso zai iya sauya lissafin siyasar Najeriya.
Ijebor ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce fitowar Obi ta gabatar da abin da ya bayyana a matsayin sabon tsarin siyasa a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Takarara Obi ta ba yan Najeriya zabi
A rahoton Vanguard, ya ce saƙon yaƙin neman zaɓen Obi ya mayar da hankali kan shugabanci mai bai wa kowa dama, ingantaccen shugabanci, ci gaba da kuma jajircewa wajen yi wa ’yan Najeriya hidima.
A cewar Ijebor, takarar Obi ta haifar da muhawara tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasa, musamman waɗanda suka yi imanin cewa zaɓen 2027 ya kamata ya bai wa masu kaɗa ƙuri’a damar tantance tarihin aiki, ƙwarewa, halayya da hangen nesa na ’yan takarar.
“Ga NDC da dimbin magoya bayanta da ke ƙaruwa, Obi ya wuce zama waninsuna kawai a takardar zaɓen shugaban ƙasa. Ana kallonsa a matsayin sabon zaɓin siyasa d zai ba masu kada kuri'a damar nazari,” in ji shi.
Kwankwaso da Obo za su bada mamaki
Ijebor ya ce sauye-sauyen kawancen siyasa da hulɗa da jama’a a matakin ƙasa na ƙara ƙamari a faɗin Najeriya yayin da jam’iyyu da ’yan takara ke shirin zaɓen 2027.
Ya bayyana haɗin Obi da Kwankwaso a matsayin wanda zai iya sauya tsarin siyasa, yana mai cewa takarar NDC ta zama wani ɓangare na sabon lissafin siyasar da ya kunno kai gabanin zaɓen.

Source: Twitter
Ijebor ya ƙara da cewa kasancewar Obi da Kwankwaso a takardar zaɓe zai bai wa masu kaɗa ƙuri’a wata kafa da za su yi la’akari da ita a takarar shugaban ƙasa..
“2027 na zuwa, ’yan Najeriya na kallo. Labarin siyasar ƙasar zai sauya,” in ji Ijebor.
Peter Obi ya amince a saki bayanansa
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya ce ba shi da wata matsala da Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta fitar da takardun digirinsa da sauran bayanan karatunsa.
Peter Obi ya ce jami’ar ta ba shi digirin BA a Falsafa a shekarar 1984, kuma ya nemi a fitar da bayanan bisa doka idan akwai buƙatar hakan.
Ya ce ba shi da wata matsala da a fitar da takardun digirinsa da sauran bayanan da suka shafi karatunsa a jami’ar.
Asali: Legit.ng

