Yan Takara 3 da Suka Sha Alwashin Dawo da Tallafin Fetur idan Aka Zabe Su
- Akwai ‘yan takarar shugaban kasa irinsu Atiku Abubakar da ke kan gaba-gaba wajen kamfe da maido tallafin fetur
- Omoyele Sowore wanda bai taba shiga cikin gwamnati ba, dama ya dade yana kokawa da tsadar mai a Najeriya
- Shi Gbenga Olawepo-Hashim ya ce zai sauke farashin fetur ne ta hanyar karfafa Naira da kuma tace mai a cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - Tuni an buga gangar siyasa ga masu burin zama shugaban kasa da kuma neman kujerun majalisun tarayya.
Zuwa yanzu kusan babu abin da masu neman mulkin Najeriya a kai suke magana kamar tallafin fetur da aka cire a Mayun 2023.

Source: Getty Images
Abin da rahoton nan ya yi shi ne tattaro wasu ‘yan takarar shugaban kasar Najeriya da suka ci burin dawo da tallafin man fetur.
‘Yan takaran da ke tare da tallafin fetur

Kara karanta wannan
Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur
1. Atiku Abubakar — ‘Dan takaran ADC
Atiku Abubakar ya dage cewa sai ya dawo da tsarin tallafin fetur ta yadda talaka zai saye mai a farashi mai rahusa.
A zaben wannan karo ne ‘dan siyasar ya koma layin nan, a baya yana cikin masu ganin rashin gaskiya ya cika tallafin.
‘Dan takaran na jam'iyyar ADC ya yi alkawari gwamnatinsa za ta hada-kai da matatun gida, ta ba su danyen mai da araha.
Tun da yanzu ana tace mai a gida, The Cable ta rahoto Atiku yana cewa za a iya samun saukin farashi a gidajen mai.
Gwamnatin Bola Tinubu da ‘yan kasuwa daga kasashen ketare sun nuna adawa da shirin, suna ganin zakin baki ne.
Babu mamaki Atiku Abubakar ya fuskanci tirjaya daga wadanda suka amfana da soke tallafin.
2. Omoyele Sowore — ‘Dan takaran AAC
Yele Sowore bai taba goyon bayan janye tallafin man fetur a Najeriya ba, a zaben 2027 ma yana nan a kan bakarsa.
Idan aka zabi jam’iyyar AAC a takarar shugaban kasa, shi kuma ya yi alkawarin zai maido tallafi a harkar man fetur.
An rahoto shi yana cewa har gobe gwamnatin tarayya tana kashe kudi domin rike farashin mai da na dala a yadda suke.
Ban da kalubalantar ikirarin daina biyan kudin tallafin, Sowore ya ce gwamnatinsa za ta sauko da farashin fetur a kasar.
Sai dai ba kamar Atiku ba, tsohon ‘dan gwagwarmayar bai iya bayani sosai game da yadda wannan shiri zai tabbata ba.
Ba a san dabarar da zai bi da yadda zai samo kudin da zai biya da kuma tsarin da zai kawo ba.
3. Gbenga Olawepo-Hashim — ‘Dan takarar Accord
Gbenga Olawepo-Hashim yana cikin masu neman takaran shugaban kasa 2027 da ke talla da sauke kudin litar man fetur.
‘Dan takaran na jam’iyyar Accord ya yi alkawarin saka tallafi a kayan mai idan ya yi nasarar shiga fadar Aso Rock.
Shi zai yi amfani da basira wajen sauke farashin na fetur, dizal da makamantansu kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Source: Getty Images
Yana da tsarin da zai ga litar man fetur ta dawo N200 zuwa N610 kuma ba tare da kudin da ake samu daga FAAC ya ragu ba.
Idan Olawepo-Hashim ya karbi mulki, ya ce zai duba adadin man da ake hakowa da kuma farashin dala domin ya rage tsadar lita.
Wani kalubale shi ne akwai rudani a jam'iyyar Accord a kan ainhin 'dan takarar shugaban kasa.
Dawo da tallafin fetur zai tsorata 'yan kasuwan waje
An samu rahoto cewa kungiyar IMPI ta yi gargadi cewa shirin dawo da tallafin man fetur na iya tsoratar da masu zuba jari daga kasashen waje.
Shugaban kungiyar, Dr Omoniyi Akinsiju, ya bayyana cewa tsarin zai rage kudin shiga tare da haifar da rashin tabbas a kasuwannin duniya.
Duk da wannan suka, wasu 'yan siyasa kamar Jonathan Vatsa na APC sun goyi bayan Atiku Abubakar na ganin man fetur ya yi araha.
Asali: Legit.ng

