Obi da Kwankwaso Sun Fitar da Kwamitin Yakin Zaben Shugaban Kasa a NDC

Obi da Kwankwaso Sun Fitar da Kwamitin Yakin Zaben Shugaban Kasa a NDC

  • NDC ta fitar da mutanen da za su yi mata kamfe domin tallata tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a Najeriya
  • An naɗa babba a tafiyar OK, John Ughulu, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen 2027
  • Sakataren kwamitin kamfen din ita ce Saadatu Sani, za ta yi aiki da kananan kwamitoci dabam-dabam a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Kungiyar siyasa ta Obi-Kwankwaso ta fitar da sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban Najeriya.

‘Yan kungiyar OK ta bayyana jerin mutum 59 da za su yi mata yakin takarar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.

Peter Obi
'Dan takaran NDC, Peter Obi a wata makarantar koyon aikin jinya Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Obi/Kwankwaso sun samu kwamitin yakin zabe

Vanguard ta ce kungiyar ta sanar da kwamitin ne a ranar Alhamis, inda ta hada masu kula da yankunan kasar nan da jihohi.

Kwamitin kamfen ya kunshi daraktocin sassa daban-daban da suka hada da sashen wayar da kan jama'a da harkokin mata.

Akwai bangarorin dabarun yakin neman zabe, tsaro, shari'a da sauran fannonin kamfe.

Kara karanta wannan

Mabiyan Sheikh Lukuwa sun kawo cikas a matakin da aka ɗauka kan taɓa iyayen Annabi SAW

John Ughulu aka nada a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen sai Saadatu Sani za ta zama Sakatare na kasa.

Ita ma Saadatu Sani tana cikin shugabannin kwamitin yakin zaben mai mutane kusan 60.

Tsarin kwamitin yakin neman zaben NDC

Kwamitin ya kunshi wakilai da-dama daga shiyyoyi shida na Najeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja a cewar jaridar PM News.

Haka zalika jerin yana dauke da masu kula da harkokin ƙungiyar a dukkan jihohi 36.

Cikin wadanda aka nada akwai Suleiman Abubakar, mai kula da Arewa ta Tsakiya; Hashimu Dungurawa, Arewa maso Yamma.

A Arewa maso Gabas an zabi Amadu Gwambe, sai Dr Adebayo Adefolaseye zai kula da jihohin da ke yankin Kudu maso Yamma.

Sai Christopher Ighodaro a Kudu maso Kudu da El-Shaddai Ikeh a Kudu maso Gabas.

Sabo Gashua da fasto suna cikin kwamitin kamfe

Haka kuma jam’iyyar NDC ta nada Rabaren Mike Agbon a matsayin Daraktan hulda tsakanin kabilu a shiyyar Arewacin Najeriya.

Sabo Gashua ya zama Daraktan tattara kungiyoyin magoya baya a matakin ƙasa, Glory Adayi ita ce mai kula da harkokin mata.

Kara karanta wannan

Shettima ya yi magana da aka fahimci kalamansa a baibai kan Tinubu

Kabir Yahaya ne mai kula da hulɗa da masu ruwa da tsaki akwai Abdumumini Tijjani zai kula da F tattara magoya baya.

Daraktan harkokin shari'a shi ne kingdom Okere sai Abiodun Dabiri a matsayin Daraktan tsare-tsare da dabarun yaƙin neman zaɓe.

Tsohon ‘dan sanda, Richard Enemona shi ne Daraktan tsaro da leƙen asiri, Aisha Abdulrahaman ta zama Daraktar gudanarwa.

Sauran ‘yan kwamitin kamfen sun haɗa da Yusuf Mani, Peace Daful, Farfesa Charles Nwekeaku da kuma Sunmisola Adebayo.

Saadatu Sani ta taya su murnar samun wannan matsayi, ta nemi su tallata manufofin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ga al’umma.

Peter Obi
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso masu takara a NDC Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Aisha Buhari ta ziyarci Atiku Abubakar

Siyasa ta shigo har an ji labari jama’a suna ta maganganu da aka ga Aisha Buhari a gidan Atiku Abubakar mai neman takara a jam'iyyar ADC.

Tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, tare da mutanenta sun kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran adawa.

A lokacin ziyarar, Atiku ya nuna damuwarsa game da matsin lamba da halin kunci da 'yan Najeriya ke ciki sakamakon manufofin gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng