Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Faɗi Wanda Yake Hangen Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2027

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Faɗi Wanda Yake Hangen Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2027

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya yi hasashen jam'iyyar da zata lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Honorabul Benjamin Kalu ya ce ya zama wajibi masu ruwa da tsakin APC na Abia su haɗa kansu domin tunkarar babban zaɓe na gaba
  • A cewarsa tun da safe ake kama fara don haka ya kamata su fara shiri domin APC ce zata yi gabala a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kalu, ya bayyana kwarin guiwar cewa jam'iyyar APC zata sake samun galaba a zaben shugaban kasa na 2027.

Kalu ya ce ƴan Najeriya da dama daga lungu da saƙo na kan hanyar shiga jam'iyya mai mulki tun kafin babban zaɓe na gaba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata, ya sanya dokar kulle a garuruwa biyu bayan faɗa ya kaure

Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kalu.
Benjamin Kalu Ya Ce Jam'iyyar APC Ce Zata Sake Lashe Zaɓen Shugaban Kasa a 2027 Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Abia wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zama wajibi mu haɗa kanmu - Kalu

Da yake jaddada muhimmanci haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsakin APC a Abiya, Kalu ya ce haɗin kai ne matakin farko na lashe kowane irin zaɓe.

Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyan ya kuma yi kira ga dukkan ƴaƴan jam'iyyar da su yafe wa juna kuma su hanzarta sulhunta kansu.

Kalu ya ce:

"Ina tabbatar muku APC za ta sake samun nasara a 2027, don haka ya kamata mu fara shiri tun yanzu, duk wanda aka yi wa ba daidai ba, muna rokonsa dan Allah ya yi haƙuri.
"Guguwar sauya sheƙa na nan tafe, kowa magana yake a kanmu, saboda haka halayen da zaku nuna ga sabbin mambobin da zasu shigo yana da matuƙar amfani. Dan Allah mu gyara."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

A cewarsa, ya zama wajibi kowa ya maida wuƙarsa kube, su yi aiki kafaɗa da kafaɗa domin ci gaban jam'iyyar APC, jihar Abiya da kuma ƙasa baki ɗaya.

An Nemi Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Tsige Wasu Ministoci

A wani rahoton kuma Wata ƙungiya ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya sa gilashin ba sani ba sabo, ya kori duk ministocin da suka gaza kataɓus.

Ƙungiyar BAVCCA ta kuma ayyana cikakken goyon baya ga gwamnatin Tinubu bisa aiwatar da tsarin dokar man fetur PIA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel