Tinubu Ya Nada Abdulaziz Yari a matsayin Darektan Yakin neman Tazarce a APC
- Abdulaziz Yari, shi ne Darakta Janar na kwamitin zaben Bola Tinubu, sai gwamna Hope Uzodimma a matsayin Sakatare
- Shugaba Bola Tinubu ne shugaban majalisar, yayin da Kasim Shettima da Nentawe Yilwatda ke mataimakan shugaba
- Godswill Akpabio, Tajudeen Abass, da Mai Mala Buni za su jagoranci tafiyar kamfen a shiyyoyin Kudancin da Arewacin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada kwamitin da zai taya shi yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya.
A safiyar Asabar aka ji cewa Sanata Abdulaziz Yari zai jagoranci yakin zaben Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a 2027.

Source: Getty Images
Sanarwar nada kwamitin yakin zaben Bola Tinubu
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya sanar da haka a shafin X dazu nan.
Sanatan Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari zai zama Darekta Janar yayin da Gwamna Hope Uzodinma shi ne sakatarensa.
Bola Tinubu da Kashim Shettima su ne shugaba da mataimakin shugaba na kwamitin.
Shugaban na APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda shi ma Mataimakin shugaba ne.
Mataimakan sakatarorin yakin zaben su ne Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman. Kwamitin na kunshe da majalisar mashawarta.
Majalisar ba shugaban kamfe shawara
Masu bada shawarar sun hada da: Bisi Akande, Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha da tsohon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu.
Mace guda da ke cikin mashawartan shugaban ita ce Sanata Florence Ita Giwa.
Shugaban majalisa, Godswill Akpabio, Tajuddeen Abbas da Gwamna Mai Mala Buni su ne Mataimakan DG a yankin Arewa da Kudu.
Shugaban yakin zabe a yankunan nan biyu su ne Sanata Jibril Barau da Bamidele Opeyemi.
Sauran Darekta Janar a yakin neman zaben Tinubu
Adams Oshiomhole ya samu kujerar Darekta Janar a bangaren tattaro jama’a, James Abiodun Faleke yana Darekta na harkar tsare-tsare.
Wani Darekta Janar din shi ne Femi Gbajabiamila, zai kula da bangaren gudanarwa.

Kara karanta wannan
"Na bar su da Allah"; Mataimakin gwamnan Kebbi ya yi maganar cire shi takara a 2027
Hon. James Faleke zai yi aiki kafada-da-kafada da shugabannin sassan kamfe irinsu Olushola Adeyeye, Dr Ngozi Olejeme da Uche Ekwunife.
Ragowar su ne Muntaqha Rabe, Ahmed Muhammed Ketso da Sanata Sani Danladi daga Arewa.
Matasa, lauyoyi da 'yan jarida sun shiga kwamitin
Kwamitin ya kunshi Stella Okotete, Engineer Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori a matsayin sakatarorin shirye-shiryen yakin zaben.
Akwai masana shari’a irinsu Muiz Adeyemi Banire, Dr Liman Hassan and Babatunde Ogala, Prince Lateef Fagbemi SAN da Ibrahim Shema.
Ministan labarai, Mohammed Idris Malagi zai jagoranci sha’anin shadarwa tare da Dele Alake, Bayo Onanuga da Malam Lanre Issa-Onilu.
A nan akwai Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala, da Felix Morka da kuma bangaren Abdulaziz AbdulAziz da wasu mutum uku.
Mutane biyar za su yi magana a madadin kwamitin yakin zaben tun daga Dele Alake zuwa Alwan Hassan da Ayobami Oyalowo.
Ragowar su ne Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda kamar yadda sanarwar ta fada.
Kudin da aka kashe a kamfe ya kai N100bn
An ji labarin yadda aka manta da dokar zabe da jam'iyyun APC da Accord suka kashe kudi sama da ₦100bn a zaben gwamnan jihar Osun.
Jam'iyyar APC ta biya wakilanta ₦100,000 a kowace rumfa yayin da Accord ta biya ₦20,000. Bayan haka, an biya jami'an tsaro da suka yi aiki.
Jam'iyyun sun kashe miliyoyin naira wajen bai wa jami'an tsaro (Yan sanda, NSCDC, da FRSC) kudi tsakanin ₦80,000 zuwa ₦100,000 a ko ina.
Asali: Legit.ng

