Yayin da Bincike Ke Ƙara Zurfi, Tsohon Gwamna Ya Magantu Kan Zargin Juyin Mulki

Yayin da Bincike Ke Ƙara Zurfi, Tsohon Gwamna Ya Magantu Kan Zargin Juyin Mulki

  • Tsohon mataimakin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya musanta rahotannin da ke danganta shi da zargin shirya juyin mulki a Najeriya
  • Julius Bokoru, mai taimaka wa Sylva kan harkokin yada labarai, ya ce yadda ake wallafa zargin na iya nuna wani yunkurin karfafa labari guda
  • Bokoru ya bukaci kafafen yada labarai su bambanta tsakanin zargi da hujja, yana mai cewa maimaita zargi ba ya mayar da shi gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva da ake zargi da hannu a juyin mulkin Bola Tinubu ya yi magana kan zarge-zargen.

Julius Bokoru, mai taimaka wa tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, kan harkokin yada labarai, ya nuna damuwa kan rahotannin zargin.

Tsohon gwamna ya wanke kansa kan zargin juyin mulki
Tsohon gwamnan Bayelsa da ake zargi a juyin mulki, Timipre Sylva. Hoto: Timipre Sylva.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce har yanzu bai samu damar tuntubar Sylva ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamntin Tinubu na neman 'ƙaryata' rahoton da ƙasar Amurka ta fitar kan Najeriya

Ana zargin yan jaridu ya wuce gona da iri

Bokoru ya ce wasu rahotannin kafafen yada labarai sun wuce iyakar binciken jarida, inda suka fara bayyana kamar suna karfafa wani labari.

Sai dai ya jaddada cewa bayaninsa ba ya nufin sukar aikin jaridun bincike, wanda ya ce yana da muhimmiyar rawa wajen kare dimokuradiyya.

Bokoru ya ce, “A mafi kyawunta, aikin jaridun Najeriya ya taka rawar gani wajen rike gwamnati, hukumomi da masu karfi da alhaki.”

Sai dai ya bukaci ‘yan jarida da kungiyoyin kafafen yada labarai su binciki tushe da hanyoyin samun bayanan da suke amfani da su kafin wallafa su.

Ya ce, “An sha jera, sake tsara da kara yada zarge-zargen ta yadda hakan ke kara ba da tunanin cewa akwai wani shiri na musamman.”

Bokoru ya kuma tambayi inda wasu bayanan da ake amfani da su wajen rahotannin suka fito da kuma lokacin da aka fara fitar da su.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya

Ya ce, “Daga ina wadannan bayanai suke fitowa? Wa ke samar da su? Me ya sa takardun bincike masu muhimmanci suke fitowa sannu a hankali?”

Ya kuma tambayi dalilin da ya sa kusan kowane sabon rahoto yake kara karfafa irin wannan zargi kan Sylva, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da shi ba.

Bokoru ya ce ba ya zargin wata kafar yada labarai da daukar nauyin wani mutum ko kungiya, saboda babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.

Sai dai ya ce tsarin rahotannin yana kara haifar da tambayar ko wasu kafafen yada labarai suna bin bincikensu ne, ko kuma suna aiki bisa wani shiri.

Ya ce, “Zan bayyana karara cewa tsarin rahotannin yana kara haifar da tambayar ko wasu kungiyoyi suna bin labaransu ne ko kuma suna aiki bisa rubutun wani.”

Bokoru ya jaddada cewa bai kamata a gabatar da zarge-zargen da ke cikin takardun bincike a matsayin tabbatattun hujjoji ba.

Ya ce, “Akwai muhimmin bambanci da bai kamata a gauraya ba: zargi ba hujja ba ne; ra’ayin mai bincike ba hukunci ba ne.”

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Ya kuma ce duk wani zargi kan Sylva ya kamata a gwada shi ta hanyar doka, inda kotu ce kadai za ta iya tantance laifi.

Bokoru ya bukaci masu son rahoto kan lamarin su bar duk wata hujja da ake da ita a kan Sylva ta fuskanci cikakken bincike.

Ya ce idan akwai isasshen dalilin gurfanar da Sylva, hukumomin da abin ya shafa su kai lamarin kotu domin a yi masa shari’a.

Bokoru ya ce a irin wannan yanayi babu damar yin tambayoyi ga masu gabatar da hujjoji ko kuma gwada sahihancin bayanan ta hanyar shari’a.

Ya kuma nuna damuwa cewa wasu takardun bincike na sirri na iya kasancewa suna fita zuwa kafafen yada labarai domin tsara ra’ayin jama’a, cewar Daily Post.

A cewarsa, idan hakan na faruwa, kafafen yada labarai ya kamata su tambayi kansu ko suna gudanar da bincike mai zaman kansa ko kuma suna taimakawa wata dabarar yada bayanai.

Ya ce aikin jaridun Najeriya shi ne su kasance masu zaman kansu, ba tare da la’akari da karfi ko matsayin wadanda ke ba su bayanai ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nuna rashin imani da suka kai hari gidan basarake ɗan shekara 90

Bokoru ya gargadi kafafen yada labarai cewa maimaita zargi sau da dama ba ya mayar da shi hujja ko gaskiyar da aka tabbatar.

Juyin mulki: Yadda aka raba N700m

An ji cewa masu bincike sun zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da gudunmuwar kuɗi domin yunkurin juyin mulkin 2025 ta hannun wani kamfani.

Rahotanni sun ce an raba sama da N700m ga jami'an soja, malamai da wasu fararen hula bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji.

Ana zargin kuɗaɗen sun ci gaba da fita har bayan kama jagoran yunkurin juyin mulkin da jami'an kasar nan suka yi a ranar 29 ga Satumban 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.