Osagie Ize Iyamu ya jarraba sa’a a 2016 da 2020, bai dace ba duk da ya sauya-sheka

Osagie Ize Iyamu ya jarraba sa’a a 2016 da 2020, bai dace ba duk da ya sauya-sheka

- Osagie Ize Iyamu ya sake shan kashi a zaben Jihar Edo wannan karo

- Kamar dai a zaben 2016, ‘Dan takarar ya gaza doke Godwin Obaseki

- Shekaru hudu da su ka wace, Obaseki ya na APC, Ize Iyamu ya na PDP

Mun tsakuro maku labarin Fasto Osagie Ize Iyamu, ‘dan takarar APC da ya sha kashi a zaben jihar Edo da aka yi a karshen makon da ya wuce.

Da sakamakon wanan zabe, wannan ya na nufin wannan Bawan Allah ya yi takara a Jam’iyyar APC da PDP, amma duk bai iya samun nasara ba.

A shekara hudu, Osagie Ize Iyamu ya nemi kujerar gwamna a PDP, ya sha kashi, sannan ya sauya sheka zuwa APC, inda nan ma ya sake shan kashi.

Osagie Ize Iyamu mai shekara 58 ya rike shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Edo a karkashin gwamna Lucky Nosakhare Igbinedion.

KU KARANTA: Abin da Melaye ya fada game da Oshiomhole da Tinubu kan zaben Edo

A 2003 Osagie Ize Iyamu ya zama sakataren gwamnatin Edo, ya rike wannan mukami har 2007.

Daga baya Osagie Ize Iyamu ya shiga jam’iyyar ACN, har ya zama mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (na reshen Kudu maso kudancin Najeriya).

A 2012 Osagie Ize Iyamu ya zama shugaban yakin neman zaben Adams Oshiomhole a jihar Edo, bayan gwamnan ya zarce sai kuma ya yi watsi da shi.

Daga baya ‘dan siyasar ya sake sauya-sheka zuwa PDP, ya zama jagoran tazarcen Goodluck Jonathan da Namadi Sambo a zaben shugaban kasa na 2015.

KU KARANTA: Abubuwan da su ka taimakawa Obaski wajen doke APC a Edo

Osagie Ize Iyamu ya jarraba sa’a a 2016 da 2020, bai dace ba duk da ya sauya-sheka
Osagie Ize Iyamu wajen kamfe
Source: Twitter

A jam’iyyar PDP mai hamayya ne Osagie Ize Iyamu ya tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Edo a zaben 2016, amma ya zo na biyu da kuri’a 253, 173.

A karshen 2019 sai aka ji cewa Ize-Iyamu ya tattara ya bar PDP, tsohon sakataren gwamnatin ya ce ya koma jam’iyyar APC ne saboda rikicin cikin PDP.

Ize-Iyamu ya yi nasarar samun tutar jam’iyyar APC a 2020, amma wannan karo ma bai dace ba.

A jiya Legit.ng Hausa ta kawo maku abubuwan da ya kamata ku sani game da rayuwar Gwamna Obaseki tun daga haihuwarsa, karatu zuwa shiga siyasa.

Obaseki ya gwabza Osagie Ize-Iyamu sau biyu, kuma a kowane zabe ya samu galaba a kan shi a kananan hukumomi 13, inda Ize-Iyamu ya yi nasara a biyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel