Osun 2026: Muhimman Abubuwa 8 da Ya Kamata kowane Mai Katin Zabe Ya Sani
Osun, Nigeria - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamnan jihar Osun a yau Asabar, 15 ga Agustan 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ana ran miliyoyin masu zabe za su fito domin tantance wanda zai jagoranci jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya a tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Source: Facebook
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dauki alkawarin gudanar da zabe mai inganci, sahihi kuma cikin kwanciyar hankali.
Gwamna Ademola Adeleke na neman tazarce ne a karkashin inuwar jam'iyyar Accord, amma yana fuskantar gogayya mai tsauri daga 'yan takara 13 na sauran jam'iyyun siyasa.
Gabanin fara wannan zabe, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata kowane mai kada kuri'a a jihar Osun ya sani. Ga su kamar haka.
1. Adadin masu zabe
Hukumar INEC ta yi rajistar mutane 2,339,233 da suka cancanta da yin zabe, wadanda aka rarraba a daukacin runfunan zabe 3,763 da ke fadin kananan hukumomi 30 na jihar Osun.
INEC ta bayyana ranar Alhamis da ta gabata cewa sama da katunan zaɓe (PVCs) miliyan 1.9 aka karɓa domin zaɓen gwamnan jihar, cewar rahoton Daily Trust.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya ce adadin ya fito ne daga cikin jimillar masu rajista 2,339,233.
2. Yan takara 14 za su fafata
Jimillar jam'iyyu 14 da 'yan takararsu ne za su fito a takardar zabe domin fafatawa a tsakaninsu a zaben gwamnan jihar Osun.
To sai dai uku daga cikin waɗannan yan takarar ne ake hasashen fafatawar za ta fi zafi a tsakaninsu kuma za su fi daukar hankalin a'umma.
Wadannan yan takara sun hada da shi kansa Gwamna Adeleke na jam'iyyar Accord, Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC da kuma Najeem Salaam na jam'iyyar ADC.

Source: Twitter
4. An kammala yakin neman zabe
Daukacin 'yan takara 14 sun samu damar gudanar da yakin neman zabensu a fadin jihar har zuwa ranar Alhamis, 13 ga Agustan 2026.
Tun farko, INEC ta kayyade wannan rana ta 13 a Agusta a matsayin ranar da za a rufe damar yakin neman zabe, gabanin lokacin fita kada kuri'a a zaben gwamnan Osun.
5. Sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, gabanin fara zaben, daukacin 'yan takara 14 sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
An gudanar da taron rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ne karkashin jagorancin Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, domin jaddada goyon baya ga zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
6. Amfani da fasahar zamani
A fannin fasaha kuma, INEC ta kara yawancin na'urorin tantance masu zabe (BVAS) daga 4,427 zuwa 5,130 a jihar Osun wani bangare na kokarin hukumar wajen amfani da fasahar zamani a zabe.
Haka zalika, INEC ta nunka na'urorin ajiyar ko-ta-kwana daga 664 zuwa 1,328 domin sauya duk na'urar da ta samu matsala cikin hanzari a ranar zaben don gudun tangarda.
7. Tsaurara matakan tsaro
Za a samu matakan tsaro masu tssuri a fadin runfunan zabe, inda rundunar 'yan sanda ta riga ta tura jami'ai kusan 15,000.
Haka zalika, INEC tana aiki kafada-da-kafada da sauran hukumomin tsaro domin dakile sayen kuri'u, sannan za a yi amfani da tsarin kwamitin hadin gwiwa kan tsaron zabe (ICCES).

Source: Twitter
An sa ran hakan zai ba da damar a rika tura jami'an tsaro ta hanyar yin amfani da bayanan sirri zuwa yankunan da aka gano suna da hatsarin tashe-tashen hankula.
Yayin da hankula suka koma kan Jihar Osun, 'yan Najeriya na sa ido da kyau domin ganin wanda zai yi nasarar zama gwamna na gaba da zarar sakamako ya fara fitowa.
8. Kananan hukumomi na sahun gaba
Kada a manta cewa daukacin 'yan takara guda uku da za su ja hankali a zaben na yau Asabar sun fito ne daga shiyya guda a jihar Osun, lamarin da ya sa zaben ya kasance mai matukar wahalar hasashe.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa
Bangarorin Accord, jam'iyyar APC da ADC kowannensu na ikirarin cewa shi ne zai lashe daukacin kananan hukumomi 30 na jihar.
Sai dai, kananan hukumomin da ake kallon su a matsayin na sahun gaba, Osogbo, Olorunda, Odo Otin da Ilesa East, su ne za su iya tantance ainihin wanda zai karbi ragamar Osun.
Atiku ya gargadi INEC kan zaben Osun
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya gargadi INEC da hukumomin tsaro kan yawaita jami’an tsaro a zaben gwamnan Osun, yana mai cewa zaben gwaji ne ga Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce zabe aikin farar hula ne, ba aikin soja ba, yana mai neman a tabbatar da gaskiya da adalc.
Ya ce yawan jami’an tsaro da yadda aka shirya tura su zuwa wuraren da za a gudanar da zaben na kama da shirye-shiryen yaki maimakon aikin dimokuradiyya na farar hula.
Asali: Legit.ng


