Kano Ta Sake Kafa Tarihi a Jarabawar NECO, Ta Doke Legas da Sauran Jihohin Najeriya
- Kano ta zo ta daya a sakamakon NECO na 2026, inda ɗalibai 74,413 suka samu 'credit' biyar ciki har da Turanci da Lissafi
- Wannan shi ne karo na biyu a jere da Kano ta zama ta daya a Najeriya, bayan samun irin wannan nasara a jarabawar NECO ta 2025
- Gwamna Abba Yusuf ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da zuba jari a ilimi, ciki har da tallafa wa ɗalibai marasa galihu da inganta makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jihar Kano ta zo ta daya a jerin jihohin da suka samu mafi yawan ɗalibai da suka yi nasara a jarabawar NECO ta shekarar 2026.
Sakamakon ya nuna cewa ɗalibai 74,413 daga Kano sun samu 'credit' biyar ko fiye, ciki har da darussan Turanci da Lissafi.

Source: Facebook
Jihar Legas ta zo ta biyu da ɗalibai 72,496, yayin da Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 55,543, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Kano ta sake zama ta daya
Wannan shi ne karo na biyu a jere da Kano ta jagoranci jadawalin sakamakon NECO na ƙasa. A shekarar 2025 ma, Kano ce ta samu mafi yawan ɗalibai da suka samu maki biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Gwamna Abba Yusuf, ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature, ya yabawa ɗalibai, malamai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki kan ilimi saboda wannan gagarumar nasara.
Ya ce nasarar da Kano ta samu har sau biyu a jere shaida ce cewa zuba jarin da gwamnatinsa ke yi a fannin ilimi na samar da sakamako mai auna.
“Kano ta ci gaba da kasancewa ta daya a NECO har sau biyu a jere, wanda ya sanya jihar ta zama kan gaba wajen sakamakon SSCE a shekarun 2025 da 2026,” in ji shi.
Kano ta kashe N4.4bn kan jarabawar ɗalibai
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa ilimi fifiko ta hanyar ƙara kasafin kuɗi, inganta kayan more rayuwa a makarantu da ɗaukar malamai.
Ya kuma ce gwamnati za ta ƙara horas da malamai, bayar da tallafin karatu da kuma taimaka wa ɗalibai marasa galihu.
A wani ɓangare na shirin tallafin, Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da N4.4bn a shekarar 2026 wajen ɗaukar nauyin ɗalibai da za su rubuta jarabawar kammala sakandare, musamman waɗanda ba su da hali.
Ya ce manufar shirin ita ce kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai shiga jarabawa, tare da ba su damar yin jarabawar cikin yanayi mai kyau.
Kano ta ware N405.35bn ga ilimi
Gwamnan ya ce nasarar NECO ta baya-bayan nan na daga cikin ci gaban da ɗaliban Kano suka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa.
Ya ce ilimi ya kasance fannin da ke karɓar kaso mafi yawa na kasafin kuɗin Kano a lokacin mulkinsa, wanda ya zarce ma’aunin da UNESCO ta tanada. A shekarar 2024, bangaren ilimi ya samu kusan kashi 29.95 na kasafin kuɗin jihar.
A kasafin 2025 kuma, an ƙara kuɗin ilimi zuwa N168.35bn, wanda ya kai kusan kashi 31 cikin 100 na kasafin jihar.
A shekarar 2026, gwamnatin jihar ta ware N405.35bn ga fannin ilimi, wanda ya kai kusan kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na N1.478tn.

Source: Original
Gwamnati ta kara kudin WAEC da NECO
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin jarabawar West African Examinations Council (WAEC) da National Examinations Council (NECO).
Gwamnatin ta amince da karin kudin ne zuwa N50,000 ga kowane ɗalibin sakandare, wanda zai fara aiki daga jarabawar shekarar 2027.
Asali: Legit.ng


