Sanatan APC Ya Jawo Wa Kansa, Kalamansa kan Zaben Osun Sun Jefa Shi cikin Matsala

Sanatan APC Ya Jawo Wa Kansa, Kalamansa kan Zaben Osun Sun Jefa Shi cikin Matsala

  • ’Yan sandan Osun sun gayyaci Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, domin ya yi bayani kan kalamansa da suka yadu a kafafen sada zumunta
  • Sanatan ya bukaci magoya bayan APC su “kashe” ’yan jam’iyyar Accord idan suka gan su yayin zaben gwamna da za a gudanar a wasu sassan jihar
  • Tawagar Fadahunsi ta ce kalamansa ba wai kiran tashin hankali ba ne, illa kira ne ga masu kada kuri’a su yi watsi da Accord ta hanyar amfani da kuri’u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Osogbo - Rundunar ’yan sandan jihar Osun ta gayyaci Francis Fadahunsi, sanatan da ke wakiltar mazabar Osun ta Gabas, kan kalaman da ya yi na cewa a “kashe” ’yan jam’iyyar Accord.

Gayyatar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya barke a kafafen sada zumunta kan kalaman sanatan, inda ya umurci magoya bayan APC da su “kashe” ’yan jam’iyyar Accord idan suka gan su yayin gudanar da zabe a wasu sassan jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

'Yan sanda sun gayyaci Sanata Fadahunsi a Osun
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu da Sanata Francis Fadahunsi Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 11 ga Agusta, 2026.

'Yan sanda sun gayyaci Sanata Fadahunsi

A cikin wasikar ’yan sanda sun gayyaci Fadahunsi domin ya “yi karin haske kan yanayin” da ya kai ga kalaman da ake zargin ya yi a wani gangamin yakin neman zaben APC a Ilesa ranar Talata, 11 ga watan Agustan 2026, The Punch ta kawo rahoton.

Wasikar da Samuel Etaifo Erale, kwamishinan ’yan sanda mai kula da harkokin zabe a jihar Osun, ya sanya wa hannu ta umarci Fadahunsi da ya isa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Osogbo ranar Laraba, 12 ga Agusta, da karfe 11:00 na safe.

“Gayyatar ta samo asali ne daga bayanan da rundunar ’yan sandan Najeriya ta samu, wadanda ke zargin cewa yayin jawabinka a shirin da aka ambata, ka yi kalaman da ake ganin suna da yanayin barazana, tunzura jama’a da kuma razanarwa, kuma tuni an fara yada kalaman a kafafen yada labarai da na sada zumunta,” in ji wasikar.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya jawo magana, ya bukaci masoyansa su 'kashe' abokan hamayya

‘Ina nufin a kashe su da kuri’u’

A wani bidiyo da aka wallafa a X ranar Talata, Sanata Fadahunsi na APC, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci, ya bukaci magoya bayansa su kashe ’yan jam’iyyar Accord.

“Daga yanzu, duk lokacin da kuka ga ’yan Accord, ku kashe su. Na ba ku izinin kashe su. Su ma suna da mata da ’ya’ya,” in ji Fadahunsi.

Bayan ce-ce-ku-cen da bidiyon ya haifar, Fadahunsi ya yi gaggawar janye kalamansa, inda ya ce an fahimci abin da ya fada ba daidai ba.

Tawagar sanatan ta ce kalaman da suka yadu a kafafen sada zumunta sun kasance “kira ne ga magoya baya da su yi watsi da jam’iyyar Accord da gagarumin rinjaye a akwatin zabe ta hanyoyin da suka dace, cikin lumana da bin tsarin dimokuradiyya” yayin zaben gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga Agustan 2026.

'Yan sanda sun gayyaci sanatan APC a Osun
Taswirar jihar Osun, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Davido ya kai karar korafi ga Trump kan zaben Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa Davido, ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da ƙasashen duniya su sa ido sosai kan zaɓen gwamnan jihar Osun.

Mawakin ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar tashin hankali, tsoratar da masu zaɓe da kuma katsalandan ga tsarin dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng