Makinde: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Samo Mafita ga 'Yan Adawa
- Seyi Makinde da ke takarar shugaban kasa na inuwar jam'iyyar APM, ya bayar da shawara ga 'yan adawa gabanin zaben 2027
- Dan takarar shugaban kasar na APM ya ce dole a samu adawa mai inganci domin tabbatar da dorewar dimokuradiyya
- Makinde ya bukaci a gudanar da yakin neman zabe bisa batutuwa masu ma'ana tare da gabatar da hujjoji da nasarorin ‘yan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Seyi Makinde, gwamnan Oyo kuma dan takarar shugaban kasa na Allied Peoples Movement (APM), ya yi muhimmin kira ga 'yan adawa.
Seyi Makinde ya bukaci jam’iyyun adawa su hada kai domin bai wa ‘yan Najeriya sahihin zabin siyasa a zaben 2027.

Source: Twitter
Makinde ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026 yayin babban taron kasa na APM da aka gudanar a dandalin Dr Rilwanu Sulaimanu Adamu Square da ke gidan gwamnatin jihar Bauchi, cewar rahoton The Cable.
Wane kira Makinde ya yi ga 'yan adawa?
Ya ce shugabancin jam’iyyar APM na kasa dole ne ya kasance cikin shirin yin aiki da sauran jam’iyyun siyasa domin samar da hadin kan da zai shiga zaben 2027, The Punch ta kawo labarin.
“Kamar yadda na fada, kasancewar sahihiyar adawa ce ke tabbatar da dorewar dimokuradiyya."
“Saboda haka, dole sababbin shugabanninmu su kasance cikin shirin yin aiki da sauran jam’iyyun adawa domin tabbatar da cewa mun bai wa Najeriya sahihin zabin siyasa a babban zaben 2027,” in ji Makinde.
Makinde ya bayyana bukatun Najeriya
Dan takarar shugaban kasar ya ce ‘yan Najeriya na bukatar tattalin arzikin da zai iya fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci, samar da ayyukan yi masu amfani ga matasa, ingantaccen ilimi da kuma tsaro mai inganci.
Ya ce an dade ana auna gwamnonin kasar ne da sanarwa, maimakon a duba shaidun da ke nuna yadda manufofinsu suka inganta rayuwar al’umma.
“Mun dade muna auna gwamnoninmu da sanarwa. Ana gabatar mana da manufa bayan manufa, maimakon shaidar inda wadannan manufofin suka inganta rayuwar mutane,” in ji shi.
Makinde ya ce yana son ganin siyasar da bambancin ra’ayi ba ya mayar da mutane makiya, inda adawa ba za ta kasance kawai don kawar da masu mulki ba, sai dai ta kasance hanyar gabatar da sahihiyar madadin da ya fi inganci.
Makinde ya bayar da shawarwari kan 2027
Ya kuma yi kira da a mayar da yakin neman zaben 2027 kan batutuwan da suka shafi rayuwar jama’a, inda ‘yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyu daban-daban za su gabatar da hujjoji tare da bayyana yadda za su sauya rayuwar ‘yan Najeriya idan aka zabe su.
“Bari yakin neman zaben da ke tafe ya kasance fafatawar ra’ayoyi. Bari mu tattauna kan hujjoji. Bari mu kwatanta nasarorin da aka samu.
“Bari duk wanda ke neman jagorantar ‘yan Najeriya ya amsa tambaya daya mai sauki: Ta yaya rayuwar ‘yan Najeriya za ta inganta saboda an ba mu damar yin shugabanci?” in ji shi.

Source: Facebook
Makinde ya soki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da barin darajar naira ta riƙa sauyawa a lokaci guda sun jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng


