An Yi Wa Su Kwankwaso Alkawarin Kuri'u Miliyan 10 a Zaben Shugaban Kasa na 2027
- Yan tafiyar OK Movement sun lashi takobin samar da kuri’u miliyan 10 ga tikitin Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso a zaɓen 2027
- Ƙungiyar ta ce tana da tsare-tsare a matakin rumfunan zaɓe, ƙananan hukumomi da jihohi domin tabbatar da nasarar jam'iyyar NDC
- Mataimakin daraktan-janar na OK Movement ya buƙaci NDC ta bar ƙungiyar ta ci gaba da aiki da kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mataimakin Daraktan-Janar na Obi/Kwankwaso Movement (OK Movement), Prince Abubakar Suleiman, ya ce sun shirya tsaf domin tara wa NDC miliyoyin kuri'u.
Ya bayyana ƙungiyar za ta samar da kuri’u miliyan 10 ga tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Suleiman ya bayyana hakan ne jiya a Michika, Jihar Adamawa, yayin da yake jawabi ga manyan masu ruwa da tsaki na ƙungiyar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya ya sauya sheka, ya bi tafiyar su Kwankwaso a NDC
OK Movement ta tsara tara kuri'u
Ya bayyana cewa OK Movement na da tsare-tsare masu aiki a matakin unguwanni, ƙananan hukumomi da jihohi a faɗin ƙasar, yana mai cewa ta kafa ƙaƙƙarfan tushe a tsakanin jama’a a dukkan shiyyoyin siyasa shida.
A cewarsa, ƙungiyar ta tattara ’yan Najeriya da suka yi imani da ƙwarewa da mutuncin haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso wajen ceto ƙasar nan.
“Haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso shi ne begen talakan Najeriya. Mun kammala tsara taswirarmu da kuma tattara magoya baya, kuma zan iya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za mu samar da kuri’u miliyan 10 ga wannan haɗin gwiwa,” inji shi.
An yaba wa shugaban OK Movement
Prince Suleiman ya kuma yabawa Daraktan-Janar na ƙungiyar, John Ughulu, bisa ƙoƙarinsa na ƙarfafa ƙungiyar a faɗin ƙasar.
Ya bayyana shi a matsayin jagora mai himma da mayar da hankali, yana mai cewa jajircewarsa da salon jagorancinsa na dabaru sun taimaka wajen faɗaɗa ƙungiyar zuwa sassan ƙasar tare da ƙara mata karɓuwa.

Kara karanta wannan
Kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya ta yi magana kan kama Atiku gabanin zaben 2027
Suleiman ya kuma buƙaci shugabannin jam'iyyar NDC su bar ƙungiyar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta da kanta.

Source: Twitter
Ya nemi yancin kungiyar daga NDC
Ya bayyana cewa OK Movement ƙungiya ce mai zaman kanta, kuma ba ta ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar kai tsaye.
“Muna roƙon shugabannin NDC su bar ƙungiyar ta ci gaba da kasancewa a matsayin ƙungiyar tallafa wa takara mai zaman kanta.
"OK Movement ƙungiya ce mai zaman kanta, kuma ba ta ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar NDC, Mu abokan hulɗa ne da ke aiki domin nasarar jam’iyyar, amma muna buƙatar ’yancinmu domin gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata,” in ji shi.
Babashir Lawal ya koma NDC
Kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC watanni uku bayan ya yi murabus daga ADC.
Lawal ya sanar da komawarsa jam’iyyar NDC a Abuja ranar Talata, inda ya bayyana goyon bayansa ga tikitin shugaban ƙasa na Peter Obi da mataimakinsa Rabiu Kwankwaso gabanin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng