Abin Boye Ya Fito: 'Hanyar da APC Za Ta Bi don Lashe Zaben Gwamnan Osun'

Abin Boye Ya Fito: 'Hanyar da APC Za Ta Bi don Lashe Zaben Gwamnan Osun'

  • Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana hanyar da APC za ta lashe zaben gwamnan Osun na 15 ga Agustan 2026
  • Bamidele ya ce APC ta fi hadin kai da tsari tun bayan kayen da ta sha a zaben 2022, yayin da ya ce tsarin siyasar Gwamna Ademola Adeleke ya samu tangarda
  • Sanatan ya bukaci ’yan siyasa da mazauna Osun su mutunta dokokin zabe tare da guje wa tashin hankali domin a gudanar da zaben cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya yi magana kan hanyar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta lashe zaben gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa APC za ta lashe zaben ne ta hanyar tsarin siyasarta, ba tare da dogaro da tasirin gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan

ADC: 'Abu 1 da zai hana jam'iyyar su Atiku nasara a zaɓen Osun'

APC na shiri kan zaben Osun
Sanata Opeyemi Bamidele tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Leader of the 10th Senate
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Bamidele ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026, inda ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da mazauna jihar da su tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana.

Bamidele ya hango nasarar APC

Ya yi watsi da ikirarin Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, cewa APC na dogaro da karfin gwamnatin tarayya domin kayar da shi.

Sanatan ya ce jam’iyyar ta kara samun hadin kai da tsari tun bayan kayen da ta sha a zaben 2022.

A cewar Bamidele, ingantaccen tsarin APC, tare da abin da ya bayyana a matsayin lalacewar alakar Adeleke da wasu abokan siyasarsa, sun bai wa jam’iyyar damar yin nasara.

“Sabanin shekarar 2022, APC ta Osun a yanzu ta fi hadin kai da shiri, ba wai kawai domin ta dawo da ikon siyasar jihar ba, har ma domin sake tsara ta, ta yadda za ta amfani al’ummomin da za su zo nan gaba.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya yi gargadi mai zafi ga INEC, Tinubu kan zaben Osun

“Ba za a iya fadar haka kan tsarin siyasar Adeleke ba, wanda ya shiga cikin rikici a tsakiyar wa’adinsa na farko.” In ji shi

Karfin siyasa ya fi mukami

Bamidele ya ce bai kamata a hada tsarin siyasa da kasancewa a kan mulki ba, yana mai cewa hanyar sadarwar jam’iyya a matakin kasa, karfin siyasa da alakar da take da masu zabe na daga cikin muhimman abubuwan da ke tabbatar da nasarar zabe.

“Karfin tasirin siyasa ne ke lashe zabe, ba karfin kasancewa kan mulki ba. Wannan na daga cikin manyan abubuwan da yanzu suka sanya APC cikin kyakkyawan matsayi na lashe zaben gwamna mai zuwa a Jihar Osun.” In ji shi.

Ya kawo sauya sheka da wasu jiga-jigan siyasa suka yi daga bangaren Adeleke zuwa APC a matsayin shaida kan karuwar karfin jam’iyyar.

Bamidele ya ambaci Francis Fadahunsi, sanatan da ke wakiltar Osun ta Gabas, da kuma ’yan majalisar wakilai uku, Omirin Olusanya, Wole Oke da Taofeek Ajilesoro, a matsayin ’yan siyasar da suka fice daga tsarin siyasar Adeleke. Ya ce ficewarsu ya kara karfin APC a matakin kasa gabanin zaben.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

An bukaci a guji tashin hankali

Shugaban masu rinjayen Majalisar Dattawa ya bukaci dukkan jam’iyyu da ’yan takara da su mutunta dokokin zabe tare da mayar da hankali wajen gabatar da shirye-shiryensu ga masu zabe.

"A karshe, jama’a ne, ba gwamnatin tarayya ba, za su yanke shawarar wanda zai shugabance su.” In ji shi.
Bamidele ya ce APC za ta yi nasara a Osun
Sanata Opeyemi Bamidele na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Michael Opeyemi Bamidele
Source: Twitter

Abin da zai hana dan takarar ADC rashin nasara a Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren yaɗa labaran ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan Osun, Najeem Salaam, zai yi nasara.

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa za a samu matsalar rashin nasara ne idan ba a yi zaben a cikin gaskiya da nasara kamar yadda ake fargaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng