Osun 2026: Manyan Laifuffukan Zabe a Najeriya da Hukuncin da Doka Ta Tanada

Osun 2026: Manyan Laifuffukan Zabe a Najeriya da Hukuncin da Doka Ta Tanada

Abuja – A tsarin dimokuradiyya, kada kuri'a ce hanyar da 'yan kasa ke zabar shugabannin da suke so, Najeriya ta tanadi dokoki masu tsauri domin kare tsarin zabe daga masu son yin magudi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dukkan wadannan dokoki suna cikin Dokar Zabe ta 2022, wacce ta amince da hukuncin tarar kudi ko zaman gidan yari, ko duka biyun ga duk wanda ya saba doka.

An fara zaben gwamnan Osun a Najeriya
Ya takarar gwamnan jihar Osun, Bola Oyebamiji da Ademola Adeleke da ake gudanar da zabe. Hoto: @OyebamijiBola, @AAdeleke_01.
Source: Twitter

Laifuffukan zabe da hukuncinsu a Najeriya

Rahoton hukumar INEC ya nuna cewa laifuffukan zabe suna da hadari sosai ga tsarin dimokuraɗiyya, saboda suna kuma rage amincewar jama’a ga sakamakon zabe.

Saboda haka ne hukumar INEC da hukumomin tsaro ke yawan jan hankalin ‘yan kasa su guji aikata wadannan laifuffukan zaben da ke iya jefa su gidan yari na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata kowane mai katin zabe ya sani

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin tanade-tanaden dokar zabe yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan Osun.

1. Laifin rijistar zabe sau 2 ko jabun katin zabe

Sashe na 114 na Dokar Zabe ya fayyace laifuffukan da suka shafi rijistar masu kada kuri’a, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin intanet na ofishin lauyoyi na M.A Banire & Associates.

Wadannan laifuffuka sun haɗa da yin rijista fiye da sau ɗaya, yin jabun katin zabe, amfani da sunan jami’in rijista domin yin magudi, da kuma yin rijista da sunan wani mutum.

Doka ta ce duk wanda aka kama yana da hannu a irin wannan laifi zai fuskanci hukuncin tarar N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Hakan na nufin cewa idan mutum ya taimaka wajen yin wannan laifi, ba lallai sai shi ne ya yi da kansa ba, to doka za ta hukunta shi kamar wanda ya aikata da hannunsa.

Dokokin zabe da ka iya jefa mutum a gidan yari
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Joash Amupitan, a ofishinsa da ke a Abuja. Hoto: @inecnigeria.
Source: Twitter

2. Jabun takardun takara ko sakomakon zabe

Sashe na 115 ya nuna irin laifuffukan da dan takara zai iya aikatawa wajen neman mukami. Wadannan sun haɗa da buga jabun takardar neman takara, takardar sakamako, ko takardar kada kuri’a, da kuma lalata ko mallakar takardar kuri’a ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama fasto da ya kulla sace matan wasu malaman addini a Plateau

Wanda aka samu da laifi a wannan sashe zai fuskanci tara ta N50,000,000 ko zaman gidan yari na shekaru 10 ko duka biyun.

Hukuncin yana da tsauri saboda yana shafar gaskiya da amincin sakamakon zabe gaba ɗaya.

3. Haddasa tarzoma a taron siyasa

Sashe na 116 na Dokar Zabe ya haramta duk wanda zai yi ko ya haddasa tarzoma a wajen taron siyasa, musamman idan manufarsa ita ce tayar da zaune tsaye ko hana gudanuwar taron.

Doka ta ce duk wanda aka kama yana da makami ko abin tayar da hankali a wajen taron siyasa zai fuskanci hukuncin tara na N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Wannan sashe ya ba da kariya a lokacin yakin neman zabe, inda wasu jam’iyyun ke amfani da ‘yan daba don hana abokan hamayya gudanar da taruka cikin lumana.

4. Amfani da katin zabe na wani

Sashe na 117 ya tanadi hukunci ga duk wanda ke amfani da katin zabe na wani mutum ko wanda yake da katin zabe fiye da guda daya.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji yadda ta kaya tsakanin wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC

Hakanan, duk wanda ya sayar da katin zabe, ya siya, ko ya karɓa ba bisa doka ba, to ya aikata babban laifi a karkashin wannan sashe.

Hukuncin irin wannan laifi shi ne tara har ta N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

INEC ta sha gargadin jama’a da su daina ba da katin zabensu ga wasu, ko karɓar na wani, saboda hakan yana iya kai su ga daurin shekara guda.

Ana ci gaba da kada kuri'a a zaben Osun
Sabon shugaban INEC, Joash Amupitan, ya na jawabi a ofishin hukumar a Abuja. Hoto: @inecnigeria.
Source: Twitter

5. Jefa kuri’a sau 2 ko sojan gona da wani

Sashe na 119 ya haramta kada kuri’a fiye da sau ɗaya a zabe guda, ko yin amfani da sunan wani dan kasa domin kada kuri’a.

Wanda ya aikata haka zai fuskanci tara ta N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Wannan doka tana tabbatar da adalci wajen zabe, saboda tana hana mutane suyi amfani da katin jabu ko su kada kuri’a a wurare fiye da daya.

INEC ta bullo da amfani da na'urar BVAS domin tabbatar da cewa kowane mutum ya kada kuri’a sau ɗaya kawai a kowanne zabe.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan matatun mai bayan karɓar tawagar NUPENG

Osun: Kananan hukumomi da za su yi tasiri

An ji cewa zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta ya fi karkata kan Adeleke, Oyebamiji da Salaam, wadanda duk suka fito daga Osun ta Yamma.

Osogbo, Olorunda, Ife ta Tsakiya, Ife ta Gabas, Ife ta Kudu, Odo Otin, Iwo da Ilesa ta Gabas na cikin manyan kananan hukumomin jihar.

Adeleke na dogaro da ayyukan raya kasa da karfin Ede, yayin da Oyebamiji da Salaam ke neman samun gagarumar nasara a wasu muhimman kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.