ADC Ta Yi Zargin Ana Shirin Kama Wani Babba a Jam’iyyar bayan El Rufai

ADC Ta Yi Zargin Ana Shirin Kama Wani Babba a Jam’iyyar bayan El Rufai

  • Jam'iyyar ADC ta gargadi Gwamnatin tarayya kan shirin kama sakataren jam'iyyar na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola
  • Sakataren yada labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya nemi duk wata hukuma da ke neman Aregbesola ta bi tsarin doka
  • Wannan zargi na zuwa ne lokacin da ake jin karuwar hargitsi da musayar kalamai gabanin zaben gwamnan jihar Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta ADC ta ankarar da al’umma cewa tana zargin akwai makarkashiyar cafke Rauf Aregbesola.

Jam’iyyar ADC tana ganin akwai yiwuwar a damke sakatarenta na kasa, wanda ya taba yin shekaru takwas yana gwamna a Osun.

Ogbeni Rauf Aregbesola
Wasu jami'an 'yan sanda a Najeriya sai Ogbeni Rauf Aregbesola a gefe Hoto: @ADCNig
Source: Twitter

ADC ta ce ana son kama Rauf Aregbesola

Wannan rahoto da muka samu daga shafin X ya zo ne a lokacin da kwanaki kadan suka rage a yi zaben gwamna a jihar ta Osun.

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita

Sakataren yada labaran ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ya fitar da wannan jawabi da maraicen Talata, 12 ga watan Agusta 2026.

Kakakin jam’iyyar adawar ya fito yana cewa cafke tsohon ministan cikin gidan kokari ne na kawo wa ADC matsala a zaben ranar Asabar.

Jawabin kakakin jam'iyyar ADC

A madadin ADC, Bolaji Abdullahi ya ce:

"Jam’iyyar ADC ta samu kwararan rahotannin shirin cafke Sakatarenmu na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola a kwanakin da ke gabanin zaben gwamnan jihar Osun.
"Ganin yadda gwamnatin nan ta dauko hanyar yi wa ‘yan adawa barazana da matsin lamba, ba za mu yi watsi da wannan rahoto ba.
"Ogbeni Rauf Aregbesola tsohon gwamna ne na jihar Osun, tsohon ministan Gwamnatin Tarayya kuma Sakataren jam’iyyar adawa na kasa.
"Idan wata hukumar tsaro tana da cikakken dalilin gayyatar shi, akwai tsari da aka tanada domin yin hakan."

Ido yana kan gwamnari da jami'an tsaro

Bolaji ya kara da cewa yin ram da Aregbesola bai nufin komai illa gwamnati tana neman hana shi jagorantar ADC a zaben Osun.

Kara karanta wannan

ADC ta ji kamshin hadakar 'yan adawa, ana son tsayar da dan takara 1 ya tunkari Tinubu

Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord zai nemi ya koma ofis a zaben da zai gwabza da APC da sauran jam'iyyu daga ciki har da ADC.

A yanzu da abubuwa sun yi nisa wajen daukar zafi, jam’iyyar ta ce tana sa ido a kan Gwamnatin Najeriya da kuma jami’an tsaron kasar nan.

"Duk abin da ya faru yanzu, ko a lokaci ko kuwa bayan zaben ranar Asabar za a kalle shi ne da matakin da aka dauka a yanzu ba bayanin da za a yi wa mutane bayan nan ba."

- Bolaji Abdullahi

'Yan sanda sun kama kwamishina a Osun

Ana da labari rundunar ’yan sandan jihar Osun ta kama Kwamishinan Muhalli na jihar, Mayowa Adejoorin, sakamakon zarginsa da hannu a harbe-harbe.

Jami'an tsaro sun tare motar Lexus 350 da ke dauke da kwamishinan da wani jami'in Amotekun biyo bayan wani hari da aka ce an kai wa magoya bayan APC.

Kwamitin yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke (Imole) ya soki kamen, inda yake zargin rundunar 'yan sandan da nuna son kai a jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng