Zaben Osun: 'Yan Takarar Gwamna 2 Sun Janye, Sun Mara wa Adeleke baya
- ’Yan takara biyu a zaben gwamnan Osun, Adebayo Adewale na APM da Adedamola Adebayo na PDP, sun janye daga takara a a zaben da ke take
- Adewale ya ce ya dauki matakin ne bayan tunanin zurfi da tuntubar shugabannin jam’iyya, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki
- Adedamola Adebayo ya kuma bukaci ’yan PDP da magoya bayansa su mara wa gwamna mai ci baya a zaben da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – ’Yan takara biyu a zaben gwamnan jihar Osun, Adebayo Simon Adewale na APM da Adedamola Adebayo na PDP, sun janye daga takarar tare da goyon bayan Gwamna Ademola Adeleke.
Adebayo Simon Adewale ne ya fara bayyana matakin a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis 14 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
The Cable ta kawo labarin cewa dan takarar ya ce ya yanke shawarar janyewa ne bayan tunanin zurfi da tuntubar shugabannin jam’iyya, magoya baya da masu ruwa da tsaki.
Dan APM ya janye daga takara
The Punch ta wallafa cewa Adewale ya ce matakin ba wai an matsa masa ko wata bukata ta kansa ce ta sa ya janye ba, illa dai ya fifita muradun jihar Osun a kan burinsa na siyasa.
Ya ce:
“Ni, Adebayo Simon Adewale, dan takarar gwamnan APM a zaben gwamnan Osun na 2026, bayan tunani mai zurfi da tuntubar shugabannin jam’iyya, magoya baya da masu ruwa da tsaki, na yanke shawarar janyewa daga zaben gwamnan jihar Osun."
“Wannan shawarar ba matsin lamba ko wata bukata ta kaina ce ta haifar da ita ba; a maimakon haka, zabi ne na sani na sanya muradun Osun a kan burin kaina."
Dan PDP ya hakura da takara
Shi ma dan takarar PDP a zaben, Adedamola Adebayo, ya janye daga takarar tare da bayyana goyon bayansa ga Adeleke gabanin zaben Asabar 15 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Ya ce:
“Ni, honorable Adedamola Adebayo, wanda aka fi sani da Fryo, ina bayyana goyon bayana ga Mai Girma Sanata Ademola Adeleke gabanin zaben gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026.”
“Ina kira ga dukkan ’yan PDP, magoya baya da tsarin jam’iyyar da su yada wannan matsaya cikin lumana. Ku goyi bayan bayyanar Ademola Adeleke a matsayin gwamna har zuwa shekarar 2030."
An kashe rai a Osun
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC a Osun ta zargi cewa an harbe ɗan ƙanwar Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen gwamnan jam’iyyar har lahira tare da jikkata wani bawan Allah a jihar.
Mai magana da yawun jam'iyyar APC na Osun ya ce wasu ’yan daba sun harbe Ayegbo a kusa da gidansa da ke Esa-Oke, Obokun laamarin da ya jefa yan uwa da iyalai a cikin tashin hankali.
Jam'iyya mai mulkin Najeriya ta APC ta buƙaci rundunar ’yan sandan kasar nan ta gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara samun zafin siyasa gabanin zaɓen gwamnan Osun.
Asali: Legit.ng

