Sauki Ya Zo: 'Yan Kasuwa Sun Rage Farashin Litar Man Fetur
- Kamfanin MRS ya rage farashin fetur a Legas da kewaye daga N1,370 zuwa N1,350 kan kowace lita, yayin da wasu dillalai suka rage nasu
- Farashin fetur a wasu depot ya sauka zuwa N1,303 kan kowace lita a Fatakwal, yayin da farashin ɗanyen mai na duniya ya kuma ragu
- Farashin dizal ya kasance tsakanin N1,790 zuwa N1,900 kan kowace lita, yayin da LPG ya kai N1,125 kan kilogram a Fatakwal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Masu sayar da man fetur a Najeriya sun fara rage farashin Premium Motor Spirit (PMS), wanda aka fi sani da fetur, yayin da farashin man a rumbunan ajiya ke ci gaba da sauka.
Kamfanin MRS ya rage farashin fetur a Legas da kewaye da N20 kan kowace lita, daga N1,370 zuwa N1,350.

Source: Facebook
Binciken jaridar Vanguard ya kuma nuna cewa wasu dillalan mai masu zaman kansu sun rage farashin da suke sayar da fetur zuwa N1,360, daga sama da N1,380 kan kowace lita.
Farashin fetur ya sauka a rumbunan ajiya
Raguwar farashin na zuwa ne yayin da farashin fetur a rumbunan ajiya ke ci gaba da kasa, inda ya sauka zuwa N1,303 kan kowace lita a Fatakwal, bisa sabon rahoton Daily Depot Price Intelligence na Juma’a, 25 ga Satumba 2026.
Rahoton ya nuna cewa Bulk Strategic, Masters, Sigmund da T.S.L depots a Fatakwal na sayar da PMS kan N1,303 kowace lita, wanda shi ne mafi ƙarancin farashin da aka samu a kasuwannin da aka sanya ido a kai.
A Legas kuwa, rumbunan ajiya na A.A Rano, AIPEC, Bovas, Dangote, Emadeb, Sahara da Wosbab sun kasance suna sayar da fetur kan N1,325 kowace lita.
Matsakaicin farashin fetur ya kai N1,326 a Legas, N1,318 a Calabar, N1,315 a Warri, da N1,303 a Fatakwal.
A sabon farashin N1,350 kowace lita, farashin MRS a Legas ya fi farashin rumbunan ajiya na N1,325 da ake samu wajen wasu masu kawo man a jihar da N25.
Bambancin tsakanin farashin MRS a Legas da mafi ƙarancin farashin rumbunan ajiya a Fatakwal ya kai N47 kan kowace lita.
Farashin ɗanyen mai ya ragu a duniya
Raguwar farashin man fetur a kasuwar cikin gida ta zo ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi gagarumar faduwa.
Farashin danyen mai na Brent ya ragu da dala 2.28, kwatankwacin kashi 2.14 cikin 100, daga dala 106.58 zuwa dala 104.30 kan ganga.
Haka kuma, farashin West Texas Intermediate (WTI) ya ragu da dala 1.79, wato kashi 1.89 cikin 100, daga dala 94.61 zuwa dala 92.82 kan ganga.
Raguwar ta shafi kayayyakin da ake tacewa daga mai, inda farashin fetur ya ragu da kashi 4.31 zuwa dala 3.411, yayin da iskar gas ta ragu da kashi 3.46 zuwa dala 3.183.

Source: Getty Images
Muna sayen lita sama da 1400
Wani mazaunin Danja a jihar Katsina, Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa litar man fetut ta haura N1400 a wurarensu.

Kara karanta wannan
Kaico: An kashe budurwa a gidan saurayinta kan rikicin daukar cutar ƙanjamau, HIV
"Ko jiya na sha litar man fetur a N1,430, wannan tsadar ta yi yawa gaskiya. Muna fatan Allah ya kawo mana sauki amma ana shan wuya." In ji shi.
Dangote ya fadi dalilin tsadar fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa Aliko Dangote, ya danganta tsadar fetur a Najeriya da wasu dalilai, ciki har da ci gaba da fasa-kwaurin man zuwa ƙasashe makwabta.
Dangote ya ce farashin fetur a ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya ya fi na cikin gida da kashi 30 zuwa 50 cikin 100, lamarin da ke ba masu safarar man zuwa ƙetare babbar damar samun riba.
Asali: Legit.ng

