Osun: APC na Zargin an Yi Mata Mummunan Barna ana Shirin Zaben Gwamna
- Jam’iyyar APC a Osun ta zargi cewa an harbe ɗan ƙanwar Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen gwamnan jam’iyyar, Wole Oke, har lahira
- kakakin APC na Osun ya ce wasu ’yan daba sun harbe Ayegbo a kusa da gidansa da ke Esa-Oke, Obokun
- APC ta buƙaci ’yan sanda su gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara samun zafin siyasa gabanin zaɓen gwamnan Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Jam’iyyar APC a Osun ta yi zargin cewa an bindige wani dan uwan daraktan kamfen dinta a zaben da ake shirin yi.
Ta ce an harbe Dele Ayegbo, ɗan ƙanwar Wole Oke, Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen gwamnan jam’iyyar a jihar.

Source: Twitter
Kola Olabisi, kakakin APC a Osun, ya bayyana a wata sanarwa cewa an kashe Ayegbo a Esa-Oke, ƙaramar hukumar Obokun, cewar Punch.
Ana zargin kisan dan uwan jigon APC
Olabisi ya yi zargin cewa wasu ’yan daba da ake zargin suna cikin wata mota ne suka kashe Ayegbo a wani mahadar hanya da ke kusa da gidansa, a yankin Idofin na garin.
Sanarwar ta ce:
“APC ta jihar Osun ta yi Allah-wadai da kisan Dele Ayegbo, ɗan ƙanwar Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen gwamnan jam’iyyar, Wole Oke, a Esa-Oke, ƙaramar hukumar Obokun, cikin daren Laraba, wanda tawagar ’yan daba ta Accord Party ta aikata.”
APC ta zargi ’yan daba masu goyon bayan Accord Party da kai harin, tana mai cewa sun dade suna tsoratar da mambobi da magoya bayan jam’iyyar adawa ta APC a fadin jihar.
Olabisi ya ce:
“Bayanai sun nuna cewa an harbe Ayegbo a mahadar hanya kusa da gidansa da ke yankin Idofin, a cikin tsohon garin, da ’yan daba na Accord Party da suke tafiya cikin mota.”
Ya kuma ce mutane biyu ne aka harba yayin harin, ciki har da Ayegbo wanda ya mutu nan take, yayin da aka garzaya da ɗayan wanda abin ya shafa zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin samun kulawa.
Olabisi ya bayyana kisan Ayegbo a matsayin “mutuwa ɗaya ta yi yawa”, inda ya buƙaci rundunar ’yan sanda ta gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano waɗanda suka aikata laifin.
Ya ce:
“Kisan ɗan ƙanwar Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen gwamnanmu a Esa-Oke mutuwa ɗaya ce da ta yi yawa, kuma dole ne ’yan sanda su gaggauta gano gaskiyar lamarin domin tabbatar da adalci.”
Yayin da yake yin Allah-wadai da yawaitar kashe-kashe a jihar, Olabisi ya yi zargin cewa ’yan daba masu alaƙa da siyasa sun kashe sama da mambobin APC 30.
Gwamna zai yi karar sanatan APC
Mun ba ku labarin cewa tawagar yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke ta yi barazanar kai karar Sanata Francis Fadahunsi.
Lauyan Pelumi Olajengbesi ya bukaci Fadahunsi ya janye kalaman da ya yi tare da neman gafara a bainar jama’a cikin sa’o’i 24.
Ya ce idan Fadahunsi bai cika bukatar ba, za a garzaya kotu domin neman diyyar Naira biliyan 10 saboda bata suna.
Asali: Legit.ng

